Tinubu ya kwanta jinya a asibiti a kasar Faransa, ‘bai kamu da COVID-19 ba’

Tinubu ya kwanta jinya a asibiti a kasar Faransa, ‘bai kamu da COVID-19 ba’

-Ana rade-radin an kwantar da Bola Tinubu a asibiti a kasar Faransa

-Mai magana a madadin Bola Tinubu ya musanya wannan jita-jitar

-Tunde Rahman ya ce ‘Dan siyasar ya bar Najeriya ne domin ya huta

Jaridar The Cable ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kwanta jinya a garin Faris, kasar Faransa.

The Cable ta fahimci cewa fitaccan ‘dan siyasar bai da lafiya, kuma abin ya kai an kwantar da shi a wani babban asibiti da ke kasar ta Turai.

Sai dai akasin jita-jitar da ke yawo, Bola Ahmed Tinubu bai kamu da kwayar cutar COVID-19 ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa an yi wa Bola Tinubu gwajin Coronavirus kafin ya tafi Ingila a Disamba, kuma an tabbatar cewa bai da cutar.

KU KARANTA: Amurka: Biden ya sake ba wata ‘Yar asalin Najeriya mukami

Babban jigon na jam’iyyar APC mai mulki ya bar Najeriya zuwa Ingila a watan da ya wuce ne bayan ya koka da cewa gajiya na damunsa.

A karshen makon nan ne aka wuce da ‘dan siyasar zuwa wani asibiti da ke birnin Faris, Faransa.

Mai magana da yawun bakin ‘dan siyasar, Tunde Rahman, ya musanya rade-radin cewa Coronavirus ko wata cuta ta fitar da Tinubu.

Rahman ya ce: “Labarin ba gaskiya ba ne. Asiwaju ya na da lafiya, bai dauke da kwayar cutar COVID-19. Ya yi tafiyarsa ta karshen shekara ne”

KU KARANTA: Gwamna Zulum ya bayyana abin da ya fadawa Buhari ido da ido

Tinubu ya kwanta jinya a asibiti a kasar Faransa, ‘bai kamu da COVID-19 ba’
Bola Tinubu Hoto: The Cable shafi: thecable.ng
Source: UGC

Hadimin ya tabbatar da cewa: “Wajen shirin tafiyar, ya yi gwajin COVID-19, aka tabbatar bai kamu ba Tun da aka fara cutar, ya na kaffa-kaffa.”

Mai magana da yawun Tinubu ya hakikance a kan cewa ya bar Najeriya ne domin ya huta kamar yadda ya saba duk shekara, ba jinya ta kai shi ba.

A kwanakin bayan nan ne aka ji Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ta'aziyyar rashin mahafinsa.

Bola Tinubu ya yi addu'ar Allah ya jikan Hakimin Madobi, ya ba shi gidan Aljanna Firdausi tare da fatan Allah ya ba iyalinsa hakurin jure rashinsa.

Jagoran jam'iyyar APC na kasan ya fitar da wannan jawabi ne a wata takarda da ya aikawa Kwankwaso.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel