Tinubu ya yi wa Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa

Tinubu ya yi wa Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa

- Sanata Bola Ahmed Tinubu, jagoran jam'iyyar APC na kasa ya yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta'aziyyar rashin mahafinsa

- Tinubu ya yi addu'ar Allah ya jikan Hakimin Madobi, ya saka masa gidan Aljanna Firdausi tare da fatan Allah ya bawa magabat hakurin jure rashi

- Jagoran na jam'iyyar APC ya kuma yi wa Gwamna Abdullahi Ganduje, gwamnati da al'ummar Jihar Kano ta'aziyyar rashin dansu

Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Sanata Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ta'aziyya bisa rasuwar mahaifinsa, Malam Musa Kwankwaso.

Mista Tinubu cikin wasikar ta'aziyya a ranar Litinin a Legas ya bayyana kaduwa bisa rasuwar Kwankwaso, Hakimin Madobi, a safiyar ranar Juma'a a Kano yana da shekaru 93 a duniya.

Tinubu ya yi wa Kwakwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa
Tinubu ya yi wa Kwakwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa. Hoto: @daily_nigerian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Sirrin cin galaba kan 'yan bindiga a Arewa yana Zamfara, in ji Matawalle

Jagoran na APC, wadda ya bayyana mutuwar hakimin a matsayin abu mai ciwo ya yi addu'ar Allah ya jikansa da rahama ya saka masa da aljanna Firdausi, sannan ya yi addu'ar Allah ya bawa wadanda ya bari hakuri.

"Na yi bakin cikin bisa rasuwar mahaifinka kuma Hakiin Madobi a Jihar Kano, Alhaji Musa Sale Kwankwaso.

"Rasuwar iyaye abu ne mai ciwo, ko da ko sun tsufa, ba mu taba son rabuwa da su. Hakan ya faru da ni kuma na san irin yadda abin ke ciwo," in ji Tinubu.

KU KARANTA: Gwamnan Kano Ganduje ya yi wa Sanata Kwankwaso ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa

Ya ce ya san irin yadda tsohon gwamnan ya shaku da mahaifinsa da irin amfana da ya ke yi daga gare shi.

Kazalika, Tinubu ya ce ya zama dole a yi wa Allah godiya cewa mahaifin na tsohon gwamnan ya yi shekaru masu yawa a duniya kuma ya yi wa al'ummarsa da Najeriya hidima.

Har wa yau, ya yi wa Gwamna Abdullahi Ganduje da gwamnati da al'ummar Jihar Kano ta'aziyar rashin dan su mai muhimmanci ya kuma yi addu'ar Allah ya basu ikon jure hakurin rashi.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel