Rashin tsaro: Shugaban kasa Buhari ya san bakin zaren inji Gwamna Zulum

Rashin tsaro: Shugaban kasa Buhari ya san bakin zaren inji Gwamna Zulum

-Babagana Umara Zulum ya gana da Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya

-Shugaban kasa ya yi wa gwamnan alkawari dawo masa da masu gudun hijira

-Gwamnati ta sha alwashin samar da zaman lafiya a yankin a shekara mai zuwa

A ranar Laraba, 30 ga watan Disamba, 2020, Mai girma gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jaridar Humanitarian Times ta bayyana yadda zaman shugabannin ya kankama a fadar Aso Villa.

Da yake magana game da tabarbarewar rashin tsaro da ‘yan jarida, gwamnan Borno ya ce: “Ina tunani shugaban kasa zai iya shawo kan matsalar.”

Farfesa Babagana Zulum yace ya je wajen Mai girma shugaban kasa ne domin ya roki gwamnati ta dawo da ‘yan Najeriya da suke gudun hijira a ketare.

KU KARANTA: Zulum ya rantsar da Farfesoshi a kujerar shugabannin kananan hukumomi

Ya ce: “Na zo ne in yi wa Buhari magana mai muhimmanci game da jiharmu. Musamman dawo da ‘yan kasa da ke fake a Chadi, Nijar, da kasar Kamuru.”

“Gwamnatin jihar Borno za ta hada-kai da gwamnatin tarayya wajen dawo da su cikin gaggawa.”

“Akwai bukatar mu yi wa tsaro kallo da kyau, idan Allah ya so, gwamnatin jiha za ta hada kai da gwamnatin tarayya wajen kawo zaman lafiya a Borno.”

Shugaban kasar a na sa bangare, ya amince a tattaro duk mutanen Najeriya, musamman ‘yan jihar Borno da ke makale a makwabta su dawo gidajensu.

KU KARANTA: Zulum ya dauki hoto da jama'a a kujerar ya-ku-bayi a jirgin sama

Rashin tsaro: Shugaban kasa Buhari ya san bakin zaren inji Gwamna Zulum
Shugaban kasa Buhari tare da Gwamna Zulum Hoto: Twitter Daga: @BuhariSallau
Asali: Twitter

Muhammadu Buhari ya yi wa gwamnan alkawarin sha’anin tsaro zai inganta a kaf yankin na Arewa maso gabashin Najeriya a shekarar 2021 mai zuwa.

A tsakiyar shekarar nan kun ji yadda Sanata Kashim Shettima ya fito ya na yabawa gwamnatin Babagana Umara Zulum, abin da 'yan siyasa ba su saba yi ba.

Tsohon gwamnan ya yarda cewa lallai gwamnatin Magajinsa ta na namijin aiki a jihar Borno.

Hakan na zuwa ne bayan gwamna Babagana Umara Zulum ya karasa wani aiki da aka bar masa a jihar, a dalilin haka Shettima ya rika sharara masa addu'o'i.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel