Osaremen Okolo ta na cikin wadanda suka samu shiga Gwamnatin Biden/Harris

Osaremen Okolo ta na cikin wadanda suka samu shiga Gwamnatin Biden/Harris

- Shugaban Amurka mai jiran gado, Joe Biden ya nada mukamai har 100

- Sai nan da kwanaki 30 Joe Biden zai canji Donald Trump a White House

- Daga cikin wadanda aka ba kujera a Amurka har da wasu 'Yan Najeriya

Hausawa su na cewa da zafi-zafi a kan bugi karfe, watakila wannan ya sa a Amurka har shugaban kasa mai jiran gado ya shiryawa aikin gabansa.

Joe Biden wanda zai karbi mulki a hannun Donald Trump ya nada mukamai 100 a fadar White House inji kwamitin yakin neman zaben Biden da Harris.

Da wasu sababbin nade-nade da aka yi, jaridar Punch ta rahoto cewa shugaban kasar mai jiran gado ya cin ma burinsa na zaben ma’aikata 100 na fadarsa.

Kwamitin yakin neman zaben Biden-Harris ya bayyana cewa mutanen da shugaban kasar mai jiran gadon-mulki ya yi, za su yi wa Amurka aiki da kyau.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Joe Biden mai shekara 78

Hakan na zuwa ne bayan Biden ya bada sanarwa a ranar Alhamis cewa Kathleen Hicks za ta rike kujerar mataimakiyar Ministar tsaro a gwamnatinsa.

Wani labarin farin ciki shi ne Osaremen Okolo ta na cikin sabuwar gwamnatin, Okolo ainihinta mutumiyar Najeriya ce da iyayenta suka tare Amurka.

Osaremen Okolo ta na cikin masu bada shawara wajen yakar annobar COVID-19. Kafin ita, Biden ya nada wani mai jinin Najeriya, Adewale Adeyemo.

Sanarwar da aka fitar ta nuna Okolo ta taba aiki a matsayin babbar mai bada shawara kan harkar kiwon lafiya ga ‘dan majalisar Illinois, Jan Schakowsky.

KU KARANTA: Kotun koli ta tabbatar da nasarar Joe Biden a Jihar Pennsylvania

Osaremen Okolo ta na cikin wadanda suka samu shiga Gwamnatin Biden/Harris
Osaremen Okolo Hoto: The Street Journal Daga: Twitter
Source: Twitter

Okolo ta yi Digirin ta ne a Jami'ar Harvard a shekarar 2017 a fannin tarihin lafiya da kimiyya. Okolo ta kawo tsare-tsare a lokacin da ta ke aikin majalisa.

Dama tun kwanaki kun ji cewa Joe Biden zai tafi da wasu bakakaken fata idan ya hau kan karagar mulki. Daga cikin su akwai Adewale Adeyemo.

Adewale Adeyemo zai rike kujerar karamin Minista a gwamnatin Amurka. Sannan irinsu Cecilia Rouse da Neera Tanden za su samu wuri a gwamnatin.

A kwanan nan kuma Biden ya bada sanarwar tafiya da Mista Colin Kahl a ma’aikatar tsare-tsare.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel