Kyakyawar amarya ta rasu ana saura sa'o'i 3 a ɗaura aurenta a Katsina

Kyakyawar amarya ta rasu ana saura sa'o'i 3 a ɗaura aurenta a Katsina

- Fatima Hassan Fari, wata budurwa a karamar hukumar Funtua ta Jihar Katsina da mutu awanni uku kafin daura mata aure

- Ta mutu ne misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar 2 ga watan Janairun 2021 a lokacin da ake shirin daura mata aura karfe 10 na safe

- Yan uwa da abokan arziki sun yi alhinin rasuwarta tare da bayyana halayenta na kirki a shafukan dandalin sada zumunta

Wata budurwa a ake shirin daurawa aure, Fatima Hassan Fari ta rasu a ranar da za a daura mata aure a karamar hukumar Funtua da ke Jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa Fatima ta rasu ne misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar 2 ga watan Janairun 2021, awanni uku kafin daura mata aure da aka yi shirin yi karfe 10 na safe.

An yi mata jana'iza misalin karfe 2 na ranar Asabar din bisa koyarwar addinin musulunci.

Kyakyawar amarya ta rasu ana saura sa'o'i 3 a ɗaura aurenta a Katsina
Kyakyawar amarya ta rasu ana saura sa'o'i 3 a ɗaura aurenta a Katsina. Hoto: Mallam Muhammad Sani Isah
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mata mai sana'ar wankau ta gina gidan kanta, 'yan Najeriya sun taya ta murna

Kawayenta, da 'yan uwa da sauran abokan arziki sun yi alhinin rashin ta a shafukan dandalin sada zumunta na Facebook.

Wani abokin karatunta, Mallam Muhammad Sani Isah ya bayyana marigayiya Fatima a matsayin mace mai halaye na gari tare da taimako da jin kan al'umma.

KU KARANTA: Yadda za a kawo karshen 'yan bindiga a Arewa, Gwamna Bagudu

Ga wani sashi cikin sakon ta'azziyarsa;

"Ina bankwana da abokiyar karatu na Fatima Hassan Fari, wadda ta riga mu gidan gaskiya safiyar yau zuwa aljanna inda za ta hadu da mahaifinta," kamar yadda ya rubuta.

"Innallahi wainnailaihirajiun Fatima ta rabu da mu, Allah SWT ya yafe mata kura-kurenta ya saka mata bisa ayyukan alherin da ta yi da Jannatul Firdaus. Ina mika ta'aziyya ta ga yan uwanta musamman mambobin Asacosa. Allah ya basu hakurin jure wannan babban rashin."

Sani Isah ya kuma bayyana wasu kyawawan halayenta da gaskiya da jin kan al'umma da aikata abinda ya dace koda kowa yana sabawa.

Wasu al'umma da suma suma sun yi alhinin rasuwarta.

Kyakyawar amarya ta rasu ana saura sa'o'i 3 a ɗaura aurenta a Katsina
Kyakyawar amarya ta rasu ana saura sa'o'i 3 a ɗaura aurenta a Katsina. Hoto: Mallam Muhammad Sani Isah
Asali: Facebook

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel