Mata mai sana'ar wankau ta gina gidan kanta, 'yan Najeriya sun taya ta murna

Mata mai sana'ar wankau ta gina gidan kanta, 'yan Najeriya sun taya ta murna

- Wata mata yar Najeriya mai amfani da Twitter @sparklesNmore ta yi murnar kammala gidanta da ta kwashe shekaru tana ginawa

- Yar kasuwar ta ce duk da cewa bata siya kayan kawata gida ba tukunna amma tana gode wa Allah da ya bata ikon gina gidan

- Mutane da dama sun taya da murna yayin da wani mai amfani da Twitter ya yi alkawarin siya mata labule

Wata yar Najeriya mai sana'ar wankau ta bada labarin yadda ta yi nasarar gina gidan kanta bayan kwashe shekaru tana kokarin cimma wannan burin.

A rubutun da ta wallafa a ranar Talata 29 ga watan Disamban 2020, matar ta wallafa hotunan ta a cikin gidan ta babu komai illa bishiyar Kirsimeti.

Ta bayyana cewa a halin yanzu babu kayan kayata gida ko kujeru a gidan sai dai bishiyan murnar Kirsimeti kawai.

Matar mai sana'ar wankau ta kara da cewa a halin yanzu bata riga ta saka labulle a gidan nata ba.

Ga abinda ta wallafa a nan kasa:

Ma'abota amfani da shafin Twitter sun nuna mata kauna sosai ta yadda suka rika jinjinawa kokarinta da mayar da hankali kan aikinta.

A lokacin rubuta wannan labarin daruruwan mutane suna ta tautawan game da gidan nata.

Mata mai san'ar wankau ta gina gidanta, 'yan Najeriya sun taya ta murna
Mata mai san'ar wankau ta gina gidanta, 'yan Najeriya sun taya ta murna. Hoto: @sparkelsNmore
Source: Twitter

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da mutane ke cewa:

@ofispeaks

"Ina taya ki murna. Zan so in siya miki labule a matsayin kyauta?"

@japhheth ya ce:

"Ina taya ki murna. Allah zai cigaba da sanya wa ayyukan ki albarka."

@Christine_U ya ce:

"Ina taya ki murna! Nima na kosa in sanar da irin wannan labarin da izinin Allah."

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel