Yadda za a kawo karshen 'yan bindiga a Arewa, Gwamna Bagudu

Yadda za a kawo karshen 'yan bindiga a Arewa, Gwamna Bagudu

- Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Bagudu ya ce yin adalci tsakanin manoma, makiyaya da masunta ne zai kawo karshen 'yan bindiga

- Gwamman ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin a ranar Alhamis 31 ga watan Disambar 2020

- Bagudu ya ce rukunin mutanen uku duk sun dogara kan albarkatun ruwa da kasa ne don haka akwai bukatar a rika yi musu adalci da yin sulhu tsakaninsu

Gwamna Abubakar Bagudu na Jihar Kebbi ya ce yi wa dukkanin rukunin mutane adalci wurin rabon filaye, ciki har da manoma, makiyaya da masunta ne hanyar kawo karshen 'yan bindiga a Arewa, Daily Trust ta ruwaito.

Bagudu, yayin da aka yi wata hira da shi a Arise TV, a jiya Alhamis 31 ga watan Disamba, ya ce yi wa kowa adalci shine babban abinda zai samar da zaman lafiya da cigaba, don haka, ya kamata a yi wa dukannin wadanda ke neman filaye adalci.

Yadda za a kawo karshen 'yan bindiga a Arewa, Gwamna Bagudu
Yadda za a kawo karshen 'yan bindiga a Arewa, Gwamna Bagudu. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Mata a Kano sun yi zanga kan batan yara (Hoto)

Ya ce ana iya kawo karshen hare-haren 'yan bindiga da ya samo asali saboda wariyya ta hanyar hukunta bata gari da kuma mayar da hankali kan abinda ya fi muhimmanci wato ganin babu rukunin al'umma da aka bari cikin fushi.

A cewarsa, an samar da zaman lafiya a Jihar Kebbi ne ta hanyar hada kan dukkanin rukunin mutane wuri guda tare da warware matsalolin da ke tsakaninsu, ya kara da cewa jihohi ko garurruwan da suka bulla da hanyoyin yin sulhu tsakaninsu sun fi iya magance duk wata matsala da ta taso musu.

KU KARANTA: Nasiru Kachalla: An kashe ƙasurgumin dan bindiga a dajin Kaduna

"Akwai rikici tsakanin masu wannan sana'o'in; manoma, makiyaya da masunta domin dukkansu sun dogara ne kan ma'adinai da ke wuri guda, kasa da kuma albarkatun ruwa.

"Idan ba a kula da yadda wadannan rukunin mutanen ke amfani da wannan albarkatun na bangaren noma, a kan iya samun rashin jituwa daga lokaci zuwa lokaci musamman yanzu da akwai yawaitar matsalar ta'amulli da miyagun kwayoyi da kananan makamai," in ji shi.

A wani labarin daban, Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel