Na fice daga PDP saboda jam'iyyar ta mutu, in ji Sanata Abbo

Na fice daga PDP saboda jam'iyyar ta mutu, in ji Sanata Abbo

- Sanata Elisha Abbo ya jadada cewa zai yi takarar gwamnan jihar Adamawa a 2023

- Sanatan mai wakiltan Adamawa ta Arewa ya kuma ce ya fice daga PDP ne saboda jam'iyyar ta mutu

- Ya kuma bayyana cewa ba rikicinsa da Gwamna Fintiri bane yasa ya fice daga PDP

Sanata Elisha Abbo mai wakiltar mazabar Adamawa Ta Arewa a Majalisa ta 9 ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamna a Jihar Adamawa a shekarar 2023, The Punch ta ruwaito.

Abbo wanda ya bayyana hakan a Ganye kuma ya ce ya fice daga jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ne saboda jam'iyyar ta mutu.

Na fice daga PDP saboda jam'iyyar ta mutu, in ji Abbo
Na fice daga PDP saboda jam'iyyar ta mutu, in ji Abbo. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zamfara: 'Yan bindiga sun kashe dillalin da shanu saboda yaki siyan shanun sata

A wurin gasar gano zakarun 'yan kwallon kafa da sashin matasa na kungiyar yakin neman zabensa ta shirya, mai suna Sanata Ishaku Abbo Ambassadors, (SIA Ambassadors), Abbo ya ce zai yi takarar kujerar gwamna a Adamawa.

Da aka tambaye shi ko rashin jituwarsa da gwamna Ahmad Fintiri ne ya tilasta masa barin jam'iyyar ta PDP, Abbo ya amsa da cewa, "Na fice daga jam'iyyar PDP ne saboda jam'iyyar ta mutu."

KU KARANTA: Gwamnatin Najeriya za ta ceto dan Najeriya da Saudiyya ta yanke wa hukuncin kisa

Ya ce yana daga cikin mutane masu karancin shekaru da aka zaba a matsayin sanata a wannan gwamnatin kuma matasa na koyi da shi.

Abbo dan asalin mazabar Muchalla ne daga karamar hukumar Mubi ta Arewa a Jihar ta Adamawa.

A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, ministan tsaron Najeriya, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi, ya bukaci kiristoci da su yiwa kasa addu'ar zaman lafiya lokacin bukukuwan zagayowar haihuwar Almasihu wato kirsimeti.

Janar Magashi ya mika rokon a sakon taya kiristoci murnar Kirsimeti da ya fitar ranar Alhamis 24 ga watan Disamba kamar yadda Channels Tv ta ruwaito. Kirstimeti: Ku yi wa sojoji addu'a don kawo karshen tashin tsaro, Ministan tsaro.

Ya bukaci kiristoci da su zama kamar Yesu yayin bikin haihuwar tasa ta hanyar kyautatawa yan uwansu yan Najeriya ba tare da la'akari da bambancin addini ba sannan su yi wa kasa addu'ar zaman lafiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164