Najeriya ta kashe makudan kudade wajen biyan bashi cikin watanni tara

Najeriya ta kashe makudan kudade wajen biyan bashi cikin watanni tara

- Babban Bankin Najeria ya bayyana kudaden da Najeria ta biya bashi a cikin watanni tara na shekarar 2020

- Babban bankin ya nuna damuwarsa kan yadda bashin kullum yake hauhauwa

- Asusun ba da Lamuni na Duniya ya shawarci Najeriya da a qara samo hanyoyin domin karfafa kudaden shiga

Najeriya ta kashe kusan N2tn kan biyan bashin daga Janairu zuwa Satumba 2020, a sababbin bayanan da aka samu daga Ofishin Kula da Bashin (DMO).

A ranar Alhamis din da ta gabata ne DMO ta bayyana cewa jimlar bashin da ake bin kasar ya tashi daga N1.21tn a zango na uku na shekarar da ta gabata zuwa N32.22tn a cikin karancin kudaden shiga.

Adadin bashin ya kunshi na bashin gida da na waje na Gwamnatin Tarayyar Najeriya, da gwamnatocin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, in ji DMO.

Ofishin bashi ya ce "Gwamnatin Tarayya (FGN), gwamnatocin jihohi da Babban Birnin Tarayya (FCT) duk basusukansu sun qaru saboda basusuka da suka karba don samun damar yaki da cutar COVID-19 yadda ya dace da kuma fuskantar gibin kudaden shiga," in ji ofishin bashin.

KU KARANTA: Ka samawa matasa aiki ko ayi maka juyin mulki, Father Mbaka ga Buhari

Najeriya ta kashe makudan kudade wajen biyan bashi cikin watanni tara
Najeriya ta kashe makudan kudade wajen biyan bashi cikin watanni tara Hoto: Facebook/Central Bank of Nigeria
Asali: Facebook

Bayanai na DMO da wakilin jaridar The Punch ya tattara sun nuna cewa kudin hidimar bashin kasar daga Janairu zuwa Satumba 2020 ya tsaya kan N1.99tn.

An kashe N1.53tr a kan bashin cikin gida yayin da aka kashe N467.44bn ($1.27bn) wajen biyan bashin na waje.

Sabbin bashin cikin gida sun cinye N609.13bn a farkon zangon shekarar 2020; N312.81bn a zango na biyu, da kuma N604.19bn a zango na uku.

Biyan bashin waje ya tsaya N170.60bn ($472.57m) a farkon zango; N103.62bn ($287.04m) a zango na biyu, da N193.22bn ($507.15m) a zango na uku.

An yi amfani da tsarin musayar kudi na Babban Bankin Najeriya na dala 1 a matsayin N361 wajen canza kudaden biyan bashin waje zuwa naira a zango na farko da na biyu yayin da aka yi amfani da N381 a matsayin dala 1 a zango na uku, a cewar DMO.

Kwanan nan Babban Bankin na CBN ya nuna damuwar sa kan hauhawar tsadar bashin da Gwamnatin Tarayya ke yi.

Babban Bankin na CBN, a cikin rahoton tattalin arziki na rabin shekarar 2020, ya ce yanayin bashin na Gwamnatin Tarayya ya kara takura manufofin kasafin kudi a cikin wannan lokacin, saboda kudin ruwa ya kai N1.15tn a farkon rabin shekarar 2020.

"Wannan ya nuna cewa duk da matsalar karancin kudaden shiga, wanda COVID-19 ya kara ta'azzarawa, babban kason kudin shigar Gwamnatin Tarayya an sadaukar da shi ne ga biyan bashi," in ji shi.

Babban bankin ya ce a 19.2% cikin dari, bashin-da-GDP ya nuna matsayin gwamnati na rage karfi.

Ya kara da cewa "Duk da haka, hauhawar farashin sabis na bashi ya jaddada wani halin rashin kudin shiga da ka iya nakasa sararin kasafin kudin gwamnati, da kuma manufofin bunkasarta," in ji shi.

KU KARANTA: Rashin tsaro: Fusatattun matasa sun mamaye tare da rufe tituna a Katsina

Asusun ba da Lamuni na Duniya ya ce a cikin watan Disamba cewa Najeriya na bukatar gagarumin tattara kudaden shiga - ciki har da ta hanyar manufofin haraji da inganta harkokin mulki - don samar da sarari na karin kashe-kashe ta zamantakewar jama'a da rage kasadar da ke tattare da kasafin kudi da kuma matsalar rashin bashi.

A wani labarin, Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce za ta fara rajistar sabbin mambobi tare da sabunta rajista a ranar Litinin, 25 ga watan Janairu, jaridar The Punch ta ruwaito.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Sakatare mai kula da ita da kuma Babban Kwamitin Shirye-shiryen Taro, John Akpanudoedehe, mai taken, ‘rajistar mambobi, sabuntawa, gwajin sake nuna karfin gwiwa 25 ga Janairu’.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel