APC ta sanar da ranar da za a yi rajistar mambobi

APC ta sanar da ranar da za a yi rajistar mambobi

- Jam'iyyar APC ta bayyana ranar da za'a ci gaba da rajistar sababbin mambobi da sabunta tsofaffi

- Jam'iyyar ta shirya tsaf domin gudanar da aiki yadda ya kamata don cimma burin tafiyar 2023

- Hakazalika, gyaran zai shafi dukkan bangarori da matakan jam'iyyar domin bai wa mambobinta haqqoqinsu da suka dace

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce za ta fara rajistar sabbin mambobi tare da sabunta rajista a ranar Litinin, 25 ga watan Janairu, jaridar The Punch ta ruwaito.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Sakatare mai kula da ita da kuma Babban Kwamitin Shirye-shiryen Taro, John Akpanudoedehe, mai taken, ‘rajistar mambobi, sabuntawa, gwajin sake nuna karfin gwiwa 25 ga Janairu’.

KU KARANTA: Umakhihe yayi alƙawarin samar da tsari don saurin samar da wadatar abinci

Jam'iyyar a ranar 10 ga watan Disamba, 2020, ta ɗage rajistar mambobinta a duk faɗin ƙasar, sabuntawa, da sake rayarwa da aka shirya tun farko wanda za a fara ranar Asabar, 12 ga Disamba, 2020.

APC ta sanar da ranar da za a yi rajistar mambobi
APC ta sanar da ranar da za a yi rajistar mambobi Hoto: Facebook/All Progressives Change
Asali: UGC

Sanarwar ta karanta, “Mun amince da bukatar ci gaba da sasanta rikice-rikice kuma mun yanke shawarar karfafa sasantawa a dukkan bangarori domin fitowa a matsayin jam’iyya mai karfi, gabanin ‘yan majalisu da babban zaben na 2023.

“Bayan samun amincewar yin rijistar membobin jam’iyyar, yanzu CECPC ta shirya tsaf domin gudanar da aiki yadda ya kamata kuma a cikin wani rubutaccen lokaci, farawa daga 25 ga watan Janairu

“CECPC an shirya tsaf don gudanar da manyan tarurrukan jam’iyyar a dukkan matakai, ta hanyar adalci da kuma nuna gaskiya wajen zaben jami’ai ga bangarori daban-daban na jam’iyyar da za su kai ga babban taron jam’iyyar na kasa.

“CECPC na aiki don kirkirar tsarin jam’iyya mai cibiya wanda zai tabbatar da cikakken sa hannun dukkan mambobi tare da bayar da dama don karfafa amincewar mambobi, imaninsu, da tsunduma cikin dukkan ayyukan jam’iyyar.

KU KARANTA: Buhari ya kadu matuka da rasuwar Iyan Zazzau da Taliban Zazzau

“Ganin cewa lokaci yana son qure mana, CECPC tuni ta ninka kokarinta don saduwa da ayyukan da ke gabanta a shekarar 2021. Dimokiradiyya tana da karfi kamar jam’iyyun siyasar da ta samar; muna sake gina jam'iyyar mu ne domin karfafa demokradiyyar mu. Muna so mu tabbatar wa dukkan mambobinmu cewa sadaukarwar da muka yi don jagorantar aiwatar da sauye-sauyen siyasa a Najeriya ba zai canza ba."

A wani labarin, Majalisar koli ta Shari'ar Musulunci a Najeriya ta jinjinawa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i bisa rusa otel din da aka shirya banbadewa zindir makon da ya gabata.

Majalisar ta ce ire-iren wadannan laifukan ke gadarwa al'ummar Najeriya fushin Allah.

Hakazalika ta yabawa gwamnatin jihar bisa damke wadanda suka shirya bikin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel