Ka samawa matasa aiki ko ayi maka juyin mulki, Father Mbaka ga Buhari

Ka samawa matasa aiki ko ayi maka juyin mulki, Father Mbaka ga Buhari

- Fada Mbaka ya yi hasashen cewa da yiwuwa a kwace mulki hannun Buhari idan bai tashi tsaye ba

- A cewarsa, wadanda ke kan ragamar mulki sun yi debi kudin Najeriya fiye da yadda ake tsammani

- Malamin ya ce Ubangiji na fushi da wadannan shugabannin kuma bala'i zai fado musu udan basu canza ba

- Ya yi gargadi cewa kada wannan yayi masa raddi kan wadannan hasashen da yayi ko kuma bala'in ya fara shi

Wani malamin cocin Katolika, Rabaran Ejike Mbaka ya yi hasashen cewa za'a kawo karshen mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

Mbaka ya bayyana hakan ne a taron tarban sabuwar shekarar da ya saba yi kowace shekara a cocinsa ta Adoration Ministries dake jihar Enugu.

Ya ce wajibi ne shugaban kasan ya tashi tsaye ya ceci gwamnatinsa.

The Nation ta ruwaito Malamin da shawartan gwamna Buhari cewa ta samar da aikin yi kafin matasan Najeriya su tayar da tarzoman da kawo karshen mulkinsa.

Yace: "Ruhin ubangiji ya umurceni in gargadi gwamnatin yau cewa tayi a hankali ; ta canza salon mulkinta kuma ta kula da matasa ba tare da siyasantar da halin da suke ciki ba."

"Gwamnati ta tashi tsaye ta samar da aikin yi da zai amfani matasan kasar saboda sun ji jiki sosai."

"Kada ku siyasantar da halin da matasa ke ciki, idan ba haka, za su tashi tsaye ku su kawo karshen gwamnatin."

"Idan gwamnatin ta ko yin hakan cikin gaggawa, matasa zasu yi fito-na-fito da gwamna, kuma idan akayi kokarin hanasu, karshen gwamnati ya zo."

KU KARANTA: Jami'an yan sanda sun dakile harin yan bindiga, sun ceto wanda aka sace

Ka samawa matasa aiki ko ayi maka juyin mulki, Father Mbaka ga Buhari
Ka samawa matasa aiki ko ayi maka juyin mulki, Father Mbaka ga Buhari Hoto: Presidency
Asali: UGC

DUBA NAN: Dan sandan da ya ki karban cin hancin N864m na shawaran ajiye aiki saboda rashin adalci

A bangare guda, jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta ce za ta fara rajistar sabbin mambobi tare da sabunta rajista a ranar Litinin, 25 ga watan Janairu.

Jam’iyyar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da Sakatare mai kula da ita da kuma Babban Kwamitin Shirye-shiryen Taro, John Akpanudoedehe, mai taken, ‘rajistar mambobi, sabuntawa, gwajin sake nuna karfin gwiwa 25 ga Janairu’.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng