Rashin tsaro: Fusatattun matasa sun mamaye tare da rufe tituna a Katsina

Rashin tsaro: Fusatattun matasa sun mamaye tare da rufe tituna a Katsina

- Matasa fusatattu daga kauyukan karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina sun mamaye tituna

- Sun fito zanga-zanga sakamakon tsanantar rashin tsaro a yankunansu tare da al'amuran 'yan bindiga

- Sun tabbatar wa da gwamnati cewa idan bata dauka mataki ba za su kawo hanyoyin bai wa kansu kariya

Fusatattun matasa a jihar Katsina a jiya sun fito zanga-zanga tare da rufe manyan tituna sakamakon fusata da garkuwa da mutane tare da harin 'yan bindiga a kauyukansu.

Matasan da suka fito daga kauyuka daban-daban na karamar hukumar Dandume sun rufe babban titin da ke hada yankin da karamar hukumar Funtua ta jihar.

A ranar lahadi jaridar Daily Trust ta gano cewa matasan sun mamaye titin inda suka yi barazana ga gwamnati a kan ta dauka mataki ko kuma su samo hanyar kare kansu.

Rashin tsaro: Fusatattun matasa sun mamaye tare da rufe tituna a Katsina
Rashin tsaro: Fusatattun matasa sun mamaye tare da rufe tituna a Katsina. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Dalla-Dalla: Sojin saman Najeriya sun kai farmaki maboyar ISWAP, sun halaka 'yan ta'addan

Wani mazauni kauyen Mahuta wanda ya shiga zanga-zangar, ya sanar da cewa matasan sun fito daga kauyuka daban-daban da suka hada da Mahuta da illela.

Ya ce yankunan da suka fito zanga-zangar duk inda 'yan bindiga suka saka gaba ne inda suka hada da tabbatar da cewa sama da mutane 50 nasu suna hannun 'yan bindigan.

Daya daga cikin masu zanga-zangar ya ce 'yan sanda daga yankin Funtua sun isa wurin zanga-zangar amma basu iya hanawa ba.

Duk wani yunkurin jin ta bakin ta kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsinan ya gagara.

KU KARANTA: Na halaka mahaifiyata ne saboda mayya ce, Sojan da ya tsere daga wurin aiki

A wani labari na daban, mazauna karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa sun yi kira ga gwamnati da ta inganta tsaro bayan sace 'yan mata uku da mayakan Boko Haram suka yi.

Madagali tana daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da mayakan Boko Haram suka kwace a 2014 kafin sojin Najeriya su kwato su a 2015, Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun bayyana cewa 'yan mata biyu tare da matar aure daya ne ke aiki a gona a makon da ya gabata a wani kauyen Dar yayin da wasu mutane dauke da makamai suka cafkesu. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng