Buhari ya kadu matuka da rasuwar Iyan Zazzau da Taliban Zazzau
- Mutuwar manyan jiga-jigan masarautar Zazzau biyu ya ja hankalin Shugaba Buhari
- Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa Buhari bai ji dadin afkuwar abun bakin cikin ba
- Buhari ya aika sakoon ta’aziyya ga mutanen Kaduna a kan lamarin
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna bakin ciki a kan mutuwar manyan jagorori biyu a Masarautar Zazzau, Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu da Talban Zazzau, Abubakar Pate a rana daya.
A sakon ta’aziyya da babban mai bashi shawara a kafofin watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya saki a ranar Juma’a a Abuja, Buhari ya bayyana mutuwarsu a matsayin abun bakin ciki biyu.
KU KARANTA KUMA: Prophet Nigel Gaisie ya ce Osinbajo zai zama shugaban kasar Nigeria
Ya ce:
“Mutuwar wadannan manyan jiga-jigai biyu a masarautar Zazzau ya zo mani da kadawar zuciya saboda ba a jima ba da rasuwar Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris.
“Ina mika jajena ga iyalan mamatan biyu, masarautar Zazzau, masarautar Zazzau, gwamnati da mutanen jihar Kaduna.
“Allah Ya gafarta musu, Ya karbi kyawawan ayyukansu, Ya sanya su cikin Aljanna.”
A halin da ake ciki, Shehu ya ce Shugaban kasar ya tura tawaga zuwa Fadar Sarkin Zazzau don gabatar da ta’aziyya a madadinsa, jaridar The Guardian ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Tsohon shugaban kasa IBB ya roki yan Najeriya da su yi hakuri da FG
A baya mun ji cewa masarautar Zazzau ta yi babban rashin da ba tayi irinta ba tun rasuwar marigayi sarkin zazzau, Alha Shehu Idris. Manyan masu sarauta biyu suka mutu ranar juma'a.
Yayinda Iyan Zazzau, Aminu, ya rasu a wani asibitin jihar Legas kuma aka kai shi Zaria domin jana'iza, Talban Zazzau, Iya-Pate, ya rasu ne a Zariya bayan rashin lafiyan da yayi fama da shi.
Mai martaba sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli, ya fara sanar da mutuwar Iyan Zazzau a shafin Tuwita, ranar Juma'a.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng