Rusa gidan casu: Majalisar koli ta Shari'ar Musulunci ta jinjinawa gwamna El-Rufa'i

Rusa gidan casu: Majalisar koli ta Shari'ar Musulunci ta jinjinawa gwamna El-Rufa'i

- Gwamnan jihar Kaduna ta sha yabo da suka kan ruba gidan da aka shirya casu

- Yayinda wasu ke cewa bai kamata ya rusa ba tukun, wasu sunce yayi daidai

- An damke mammalakin gidan Otel din da wadanda suka shirya taron

Majalisar koli ta Shari'ar Musulunci a Najeriya ta jinjinawa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i bisa rusa otel din da aka shirya banbadewa zindir makon da ya gabata.

Majalisar ta ce ire-iren wadannan laifukan ke gadarwa al'ummar Najeriya fushin Allah.

Hakazalika ta yabawa gwamnatin jihar bisa damke wadanda suka shirya bikin.

A jawabin da shugaban majalisar na jihar Kaduna, AbdurRahman Hassan, ya saki, ya ce ire-iren wadannan taron shaidancin ke haifar zuba da jini da ake yi ta hanyar garkuwa da mutane, fashi da makami.

"Ko shakka babu, ire-iren wadannan abubuwa ya gadar mana fushin Allah (SWT) da muke fuskanta yanzu," wani sashen jawabin yace.

"Lalacewar tarbiyyanmu ke haifar da zub da jinin da akeyi ta hanyar garkuwa da mutane, fashi da makami da sauran laifuka."

"Yayinda muke yabawa gwamnatin jihar Kaduna kan wannan abun alkhairin da tayi, muna kira da gwamnatin ta zuba ido kan sauran wuraren da ake ire-iren wadannan abubuwa a jihar, irinsu Ajagunle, dake Maiduguri Road, karamar hukumar Kaduna ta Arewa, inda akwai gidajen tsiraici."

KU KARANTA: Kuma dai: Sama da mutane 1000 sun kamu da cutar Korona ranar sabuwar shekara

Rusa gidan casu: Majalisar koli ta Shari'ar Musulunci ta jinjinawa gwamna El-Rufa'i
Rusa gidan casu: Majalisar koli ta Shari'ar Musulunci ta jinjinawa gwamna El-Rufa'i Hoto: Facebook/KASUPDA
Source: Facebook

KU KARANTA: Mambobin kungiyar mashaya rake sun gudanar da bikin shan rake a jihar Kano (Hotuna da bidiyo)

A bangare guda, hukumar yan sandan jihar Kaduna a ranar Alhamis ta bayyana wadanda suka shirya taron banbadewa zindir da aka shirya a shirya kwanakin baya.

Kwamishanan yan sandan jihar, CP Umar Muri, ya bayyana cewa an damke matasan a ranar 27 ga Disamba, 2020, bayan sun yanke shawaran gudanar da casun mai take "Casun lalaci a Kaduna" a wani otel da karamar hukumar Kaduna ta kudu.

Wadanda aka damke sune: Abraham Alber, mammalakin otel din, Umar Rufa'i da Suleiman Lemona, Daily Trust ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel