Umakhihe yayi alƙawarin samar da tsari don saurin samar da wadatar abinci

Umakhihe yayi alƙawarin samar da tsari don saurin samar da wadatar abinci

- Sabon Sakataren Dindindin ya bayyana zuwansa don kawo cigaba a fannin samar da wadatar abinci

- Babbar Sakatariya Hajiya Karima ce ta mika masa takardun miki ayyuka a taron da akayi

- Daraktan yada labarai na Ma'aikatar Noma da Raya Karkara Theodore Ogaziechi ne ya fitar da sanarwar

Sabon Sakataren din-din-din na Ma’aikatar Gona ta Tarayya, Earnest Afolabi Umakhihe, a jiya, ya yi alkawarin bude kofa ga manufofin samar da abinci cikin sauri, jaridar Vanguard ta ruwaito

Bayan ya karbi takaddun mikawa daga Babbar Sakatariya, Hajiya Karima Babaginda, wacce kuma Darakta ce a Ma’aikatar, inda ya bayyana karara cewa batun hadin kai da goyon baya daga daraktoci ba sai an sake jaddadawa ba don cimma manufofi mabanbanta na gwamnatin Buhari a bangaren noma.

Yace: “Na zo nan ne don gudanar da manufofin bayyanannu, koya daga daraktoci, kara daraja, da kuma daidaita al’amuran Ma’aikatar.

KU KARANTA: Da Mun Kasance Cikin Matsala Da Bamu Kulle Iyakokin Kasarmu Ba - Shugaba Buhari

Umakhihe yayi alƙawarin buɗe ƙofa don saurin samar da wadatar abinci
Umakhihe yayi alƙawarin buɗe ƙofa don saurin samar da wadatar abinci Hoto: @leadershipNGA
Asali: Twitter

"Batun hadin kai da goyon baya daga daraktoci ba sai an sake jaddadawa ba domin cimma manufar Shugaban kasa game da yaduwa a bangaren aikin gona."

A cewar sanarwar yayin maraba da Sakataren na Dindindin, Babbar SakatariyaHajiya Karima Babaginda, ta fada masa (Umakhihe) cewa Ma’aikatar tana da hurumin tabbatar da wadatar abinci da samar da ayyukan yi ga matasan kasar.

Ta yi alkawarin biyayya da jajircewar Daraktoci da dukkan ma'aikatan Ma'aikatar

KU KARANTA: Gombe ta biya masu filaye da kudi N873m

“Mr. Ernest Afolabi Umakhihe wanda aka haifa a ranar 5 ga Afrilu, 1964, ƙwararren Akanta ne na babban martaba, babban mai fasaha ne kuma fitaccen mai gudanarwa ne. Ya yi aiki a Ofishin Akanta Janar na Tarayya, Ma’aikatar Harkokin Waje, Ma’aikatar Tsaro, Ma’aikatar Wasanni, Ma’aikatar Kudi, Kasafin Kudi da Tsare-Tsaren Kasa da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Tarayya na kasa,” ta kara da cewa.

A wani labarin, Gwamnan jahar Kaduna El-Rufai ya ji kan wasu fursunoni 12, ya yi umurnin sakinsu

Domin murnar shiga sabuwar shekara, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi umurnin sakin fursunoni 12 daga cibiyoyin gyara hali a jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

A wata sanarwa daga Muyiwa Adekeye, mai ba E-Rufai shawara na musamman a kafofin watsa labarai da sadarwa, ya nuna cewa an yi wa wadanda suka ci moriyar shirin bisa ga shawarar kwamitin bayar da shawarwari kan afuwa.

Rabe-raben fursunonin da aka saki sun hada da fursunoni 10 wadanda ya rage watanni shida ko kasa da haka su kammala wa’adin shekaru uku da aka yanke masu, Yayinda aka yiwa mutum biyu afuwa saboda shekaru.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.