Farin cikin sabuwar shekara yayinda El-Rufai ya ji kan wasu fursunoni 12, ya yi umurnin sakinsu

Farin cikin sabuwar shekara yayinda El-Rufai ya ji kan wasu fursunoni 12, ya yi umurnin sakinsu

- A yayin bikin shiga sabuwar shekara, gwamnan jihar Kaduna ya yiwa fursunoni 12 afuwa

- A cewar Muyiwa Adekeye, mai bashi shawara na musamman kan labarai da sadarwa, Gwamna El-Rufai ya bayar da umurnin sakinsu

- Adekeye ya bayyana cewa sakin fursunonin na bisa shawarar wani kwamitin bayar da shawarwari

Domin murnar shiga sabuwar shekara, gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi umurnin sakin fursunoni 12 daga cibiyoyin gyara hali a jihar, jaridar The Cable ta ruwaito.

A wata sanarwa daga Muyiwa Adekeye, mai ba E-Rufai shawara na musamman a kafofin watsa labarai da sadarwa, ya nuna cewa an yi wa wadanda suka ci moriyar shirin bisa ga shawarar kwamitin bayar da shawarwari kan afuwa.

Rabe-raben fursunonin da aka saki sun hada da fursunoni 10 wadanda ya rage watanni shida ko kasa da haka su kammala wa’adin shekaru uku da aka yanke masu, Yayinda aka yiwa mutum biyu afuwa saboda shekaru.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa ba zan bar PDP ba, Gwamna Ikpeazu ya magantu

Farin cikin sabuwar shekara yayinda El-Rufai ya ji kan wasu fursunoni 12, ya yi umurnin sakinsu
Farin cikin sabuwar shekara yayinda El-Rufai ya ji kan wasu fursunoni 12, ya yi umurnin sakinsu Hoto: @GovKaduna
Source: Twitter

Adekeye ya yi bayanin cewa wannan hukunci ya kasance bisa karfin iko da kundin tsarin mulki ya baiwa gwamnan.

A wani labari, mun ji cewa a yayinda Najeriya ke tsaka da fuskantar matsaloli, tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati.

KU KARANTA KUMA: Fastocin kamfen din Shugaban kasa na Gwamna Bello sun mamaye unguwannin Kano gabannin 2023

Babangida wanda ya bayyana hakan a yayinda yake jawabi a wata hira da Channels Television ya bukaci yan kasa da su zamo masu hakuri.

A cewar tsohon shugaban kasar, duk abunda yayi farko zai yi karshe. Ya ci gaba da bayana cewa da zaran yan Najeriya sun zage damtse wajen aiki don cimma manufa, kowa zai ji dadi a 2021.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel