Tsohon shugaban kasa IBB ya roki yan Najeriya da su yi hakuri da FG

Tsohon shugaban kasa IBB ya roki yan Najeriya da su yi hakuri da FG

- Tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, IBB ya taya yan Najeriya murna yayinda suke bikin sabuwar shekara

- A wani sako zuwa ga yan Najeriya, tsohon Shugaban kasar ya yi kira ga al’umman kasar da su ci gaba da hakuri da gwamnati

- A cewar Babangida, ya kamata mutane su taimakawa gwamnatin tarayya wajen magance wasu matsalolin kasar

A yayinda Najeriya ke tsaka da fuskantar matsaloli, tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida (IBB) ya bukaci yan Najeriya da su ci gaba da hakuri da gwamnati.

Babangida wanda ya bayyana hakan a yayinda yake jawabi a wata hira da Channels Television ya bukaci yan kasa da su zamo masu hakuri.

KU KARANTA KUMA: Dalilin da yasa ba zan bar PDP ba, Gwamna Ikpeazu ya magantu

Tsohon shugaban kasa IBB ya roki yan Najeriya da su yi hakuri da FG
Tsohon shugaban kasa IBB ya roki yan Najeriya da su yi hakuri da FG Hoto: @Aisha.I.Babangida
Asali: Instagram

A cewar tsohon shugaban kasar, duk abunda yayi farko zai yi karshe. Ya ci gaba da bayana cewa da zaran yan Najeriya sun zage damtse wajen aiki don cimma manufa, kowa zai ji dadi a 2021.

Yayinda yake karfafa wa yan kasa gwiwar tallafawa gwamnati wajen magance matsalolin da ke da nasaba da jagoranci, Babangida ya bayyana cewa COVID-19 ya shafi duk wani bangare na gwamnatin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Fastocin kamfen din Shugaban kasa na Gwamna Bello sun mamaye unguwannin Kano gabannin 2023

Ya yi bayanin cewa annobar ya kawo kalubale ga duniya baki daya, ciki harda Najeriya.

A wani labarin, Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ja kunnen ma'aikatu da sauran hukumomin gwamnatin tarayya da ke tattara haraji da su tashi tsaye don ganin sun samar da isassun kuɗaɗen shiga.

Mataimakiyar shugaba ta musamman kan shafukan sadarwa ga shugaba Buhari, Lauretta Onochie, ce ta bayyana cewa, shugaban ya fitar da wannan gargadin ne yau 31 ga watan Disambar lokacin da ya ke rattaba hannu kan kasafin kudin shekara 2021 mai kamawa.

Bayan sa hannu a kasafin na kimanin tiriliyan ₦13.588 wanda ya zama doka, shugaban ya ce, "Muna rubanya kokarinmu don tabbatar da mun samu isassun kuɗaɗe na kasafin 2021."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng