Fastocin kamfen din Shugaban kasa na Gwamna Bello sun mamaye unguwannin Kano gabannin 2023

Fastocin kamfen din Shugaban kasa na Gwamna Bello sun mamaye unguwannin Kano gabannin 2023

- Ana sanya ran tseren neman zaben Shugaban kasa na 2023 zai kankama a shekarar nan ta 2021

- Ana kuma sanya ran cewa mafi akasarin masu neman takara za su bayyana kudirinsu a sabuwar shekarar

- Suna daya da ke ta tashi a tseren shine na Alhaji Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi

Fastocin kamfen din gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello ya billo a wasu manyan hanyoyi a jihar Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An gano fastocin da ke dauke da rubutun da ke nuna kudirin gwamnan na neman shugabancin kasa a 2023, a wasu yankunan cibiyar kasuwancin na arewa.

A cewar rahoton, fastocin basa dauke da logon kowacce jam’iyya amma akwai babban rubutu da ke cewa “Don samun chanji 2023, ku zabi Yahaya Bello a matsayin Shugaban kasa, Jumhuriyar Najeriya.”

Fastocin kamfen din Shugaban kasa na Gwamna Bello sun mamaye unguwannin Kano gabannin 2023
Fastocin kamfen din Shugaban kasa na Gwamna Bello sun mamaye unguwannin Kano gabannin 2023 Hoto: @LugardHouse
Asali: Twitter

An manna fastocin a wasu muhimman wurare a jihar, ciki harda Murtaa Muhammad Way, hanyar filin jirgin sama da kuma hanyar Sani Marshal.

KU KARANTA KUMA: Atiku Abubakar ya ce dole PDP ta hade don cimma nasara a 2023

Sauran yankunan da aka gano fastocin sun hada da hanyar Race Course, hanyar Bompai da wasu yankuna na unguwannin gidan gwamnatin Kano.

Wasu yan Najeriya a shafin Twitter sun yi sharhi a kan fastocin.

Akibu Oluwaleke Waliu ya rubuta:

“Ko kamshin tikitin hawa kujerar Shugaban kasar Najeriya ba za ka ji ba a 2023.”

Ma'aji Umar ya rubuta:

“Wannan mutumin na so ya wofantar da kudin Kogi, wani ya fada masa idan lokaci ya kure.”

Ralph Eboigie ya rubuta:

“Ko zaben fidda gwani ba zai ci ba. Gwamnan da ya kasa. Babu wani abun rubutawa game da shugabancinsa a Kogi.”

KU KARANTA KUMA: Nigeria za ta tsinci kanta dumu-dumu a cikin nasara da wadata, In ji Maharaji

A wani labarin kuma, hadimin tsohon gwamnan jihar Imo, Sam Onwuemeodo, ya bayyana abin da ya hana mai gidansa Rochas Okorocha, zuwa wani taro na APC da aka yi.

Kwanan nan wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar APC na yankin Kudu maso gabashin Najeriya sun hadu sun yi wani taro a gidan gwamnatin jihar Imo da ke Owerri.

Sam Onwuemeodo ya yi bayanin abin da ya sa Rochas Okorocha bai samu halartar wannan taro ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel