Dalilin da yasa ba zan bar PDP ba, Gwamna Ikpeazu ya magantu
- Gwamna Okozie Ikpeazu ya magantu a kan rade-radin cewa yana shirin sauya sheka
- Ikpeazu ya ce sam bai ga dalilin da zai sa ya bar PDP zuwa wata jam'iyya ba
- Ya kuma jadadda cewa sune da karfi a jihar Abia
Gwamnan jihar Abia, Okozie Ikpeazu ya bayyana cewa ba zai sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC).
Da yake watsi da rade-radin sauya shekar, ya ce batun bai da tushe saboda PDP ce jam’iyya mafi rinjaye a jihar, jaridar The Nation ta ruwaito.
Da yake magana a Umuahia, babbar birnin jihar, Ikpeazu ya ce bai ga dalilin da zai sa ya bar PDP zuwa wata jam’iyya ba.
KU KARANTA KUMA: Fastocin kamfen din Shugaban kasa na Gwamna Bello sun mamaye unguwannin Kano gabannin 2023
Ya ce: “Ban ga dalilin da zai sa na bar PDP zuwa wata jam’iyyar siyasa ba. Yadda ake murza kambun siyasa a kowani jiha ya banbanta da juna.
“A nan Abia, mutanen sun gamsu da PDP kuma ina ganin takarar Ndi Abia zai cimma nasara a karkashin inuwar jam’iyyar PDP.”
Ikpeazu ya kara da cewa: “Babu wanda ya iya gamsar dani cewa akwai wata jam’iyya a nan Abia da ta fi PDP. Ni babban dan PDP ne kuma jigo a jam’iyyar.
“Bugu da kari, ni ne mataimakin Shugaban kungiyar gwamnonin PDP. Na gwammaci na zama kwandastan mota da na zama direban motar da bata tafiya.”
KU KARANTA KUMA: Kotun daukaka kara ta fatattaki shugaban kwamitin rikon kwaryan APC a Ribas
A wani labarin, tsohon mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayar da bayani kan yadda jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta iya yin nasara a zaben 2023.
Dan siyasan wanda yayi takarar kujerar Shugaban kasa karkashin jam’iyyar ya ce doe PDP ta hade domin samun nasara a zaben 2023, Vanguard ta ruwaito.
Ya bayar da shawarar a ranar Talata, 29 ga watan Disamba, a wani taron siyasa a karamar hukumar Afikpo ta kudu da ke yankin Ebonyi ta kudu.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng