Wike ya ce bai da ikon komawa APC da sauran jam’iyyun siyasa

Wike ya ce bai da ikon komawa APC da sauran jam’iyyun siyasa

- Duk da cewar baya farin ciki da shugabancin PDP, Gwamna Wike ya ce ba zai iya komawa wata jam’iyya ba

- Gwamnan na jihar Ribas ya ce saboda haka, ba zai bari kowa ya lalata PDP ba

- A baya Wike ya zargi kwamitin NWC na PDP da haddasa rabuwar kai a tsakanin gwamnonin jam’iyyar

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya ce ba zai iya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ko sauran jam’iyyun siyasa ba.

Gwamnan na Ribas ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Legit.ng ta gano a ranar Juma’a, 11 ga watan Disamba.

A cikin sanarwar wanda hadimin labaransa, Kelvin Ebiri ya fitar, Gwamna Wike ya ce tunda bai da ikon sauya sheka zuwa APC ko wata jam’iyyar siyasa, zai ci gaba da yin abunda zai iya don tabbatar da tasirin jam’iyyar PDP.

Wike ya ce bai da ikon komawa APC da sauran jam’iyyun siyasa
Wike ya ce bai da ikon komawa APC da sauran jam’iyyun siyasa Hoto: @GovWike
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Aminan Shugaba Buhari biyu da suka mutu bayan Abba Kyari

Gwamnan ya fadi hakan ne bayan ikirarin cewa kwamitin masu ruwa da tsaki (NWC) na PDP na haddasa rabuwar kai a jam’iyyar sannan cewa basa ra’ayin tattauna yadda za a kwace mulki daga APC a 2023.

Ya ce:

“Ba zan bari kowa ya kashe PDP ba. Suna da ikon komawa APC. Ni bani dashi kuma b azan iya komawa APC ba.

“Don haka, duk wanda yayi kokarin yin wani abu don halaka PDP, ba zan kyale ka ba. Duk wani da naga cewa yana shirin halakar da PDP, ba zan bar shi ba."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daruruwan daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare a Katsina sun dawo

A wani labarin, wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Fatai Aborode, wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Oyo.

An harbi jigon wanda ya sauya sheka zuwa PDP kwanan nan a gonarsa da ke hanyar Apodun, Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta arewa a ranar Juma’a, 11 ga watan Disamba, jaridar The Cable ta ruwaito.

Olugbenga Fadeyi, kakakin yan sandan jihar Oyo da yake tabbatar da lamarin yace wasu yan bindiga hudu ne suka yi wa jigon fashi sannan suka harbe shi a yammacin ranar Juma’a.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel