Aminan Shugaba Buhari biyu da suka mutu bayan Abba Kyari

Aminan Shugaba Buhari biyu da suka mutu bayan Abba Kyari

- Masu iya magana kan ce kudi na iya maganin kowani irin matsala amma bai da iko a kan mutuwa

- Hakan ne ya kasance a kan wasu aminan Shugaban kasa Muhammadu Buhari uku

- Ga kudi, matsayi da fada aji a hannunsu, amma kuma da lokaci yayi sai rai yayi halinsa

1. Abba Kyari

Wanda ya fara rasuwa shine Shugaban ma’aikatan Shugaban kasar Najeriya, Abba Kyari. Ya rasu a ranar 17 ga watan Afrilun 2020 yana da shekaru 67.

Aminan Shugaba Buhari biyu da suka mutu bayan Abba Kyari
Aminan Shugaba Buhari biyu da suka mutu bayan Abba Kyari Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

Kyari wanda ake kallo a matsayin mai gadin Buhari da karfafa masa gwiwa, ya rasu wata guda bayan ya yi fama da cutar COVID-19.

Ya kamu da cutar a lokacin da yayi wani tafiya zuwa kasar Jamus.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daruruwan daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare a Katsina sun dawo

2. Ismaila Isa Funtua

Bayan shi a jerin makusantan Shugaban kasar da suka mutu sai Ismaila Isa Funtua. Ya rasu a ranar Litinin, 20 ga watan Yuli.

Aminan Shugaba Buhari biyu da suka mutu bayan Abba Kyari
Aminan Shugaba Buhari biyu da suka mutu bayan Abba Kyari Hoto: @pmnewsnigeria
Asali: Twitter

Ana ta rade-radin cewa wasu da aka yi wa lakabi da ‘cabal’ sune ke juya gwamnatin Buhari yadda suke so, Funtua ya kaddamar da cewa shine wannan ‘cabal’ din.

Baya ga kasancewarsa abokin Buhari, Funtua ya kuma kasance surikin Shugaban kasar.

3. Nda-Isaiah

Wata mutuwar da ta sake kunno kai a bangaren makusantan Shugaban kasar a wannan shekarar ta 2020 itace mutuwar Nda-Isaiah.

Aminan Shugaba Buhari biyu da suka mutu bayan Abba Kyari
Aminan Shugaba Buhari biyu da suka mutu bayan Abba Kyari
Asali: Twitter

Ya kasance mammalakin jaridar Leadership. Ya mutu yana da shekaru 58 a duniya a ranar Juma’a, 11 ga watan Disamba.

KU KARANTA KUMA: Halima Abubakar: Likita yar arewa da ke neman miji a shafin soshiyal midiya

A baya mun kawo cewa, Shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga bangaren labarai, abokai, da kuma yan uwan Sam Nda-Isaiah kan mutuwar shahararren jigon kasar.

Shugaban Najeriyan yayinda yake nuna kaduwa da bakin ciki kan mutuwar mawallafin jaridar na Leadershi, ya bayyana Nda-Isaiah a matsayin aboki kuma makusanci.

Legit.ng ta tattaro cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa a ranar Asabar, 12 ga watan Disamba, daga mai ba Shugaban kasar shawara a kafofin watsa labarai, Mallam Garba Shehu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng