Yanzu Yanzu: Daruruwan daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare a Katsina sun dawo

Yanzu Yanzu: Daruruwan daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare a Katsina sun dawo

- Labari da muke samu ya nuna cewa daruruwan dalibai da aka yi awon gaba da su daga dakinsu na kwana a makarantar Sanadare na Kankara sun dawo

- Mafi akasarin daliban wadanda suka dawo bayan sun shafe tsawon dare a cikin daji sun dawo ne dauke da raunuka daban-daban

- Kakakin rundunar yan sandan jihar da shugaban makarantar sun tabbatar da hakan

An tabbatar da cewar dalibai dari biyu da suka tsere don tsiratar da rayuwarsu a daren ranar Juma’a, 11 ga watan Disamba, bayan yan bindiga sun kai hari makarantar sakandare na gwamnati da ke Kankara, jihar Katsina sun dawo.

Kakakin yan sandan jihar, Gambo Isah da Shugaban makarantar, Usman Abubakar sun tabbatar da hakan ga jaridar Channels TV a ranar Asabar, 12 ga watan Disamba.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa an sace daruruwan dalibai a yayin farmakin.

Koda dai makarantar da yan sanda basu tabbatar da rahotannin sace dalibai da kisan kowa ba, Abubakar ya ce hukumar makarantar da yan sanda da gudanar da kidayan dalibai a yanzu haka.

“Yanzu ba za mu iya bayar da tabbacin adadin daliban da aka sace ba har sai zuwa nan gaba domin wasu dalibai na bayyana a yanzu haka daga jejin da ke kusa. A yanzu haka muna daukar sunaye. Wasu kuma sun tafi gidajensu ne kai tsaye inda iyayensu ke kiranmu kan cewa yayansu suna gida,” in ji Abubakar.

Da yake koro nashi jawabin, kakakin yan sandan ya ce: “abunda ya faru shine a jiya da misalin karfe 11:30 na dare, mun samu rahoton cewa yan bindiga da yawa dauke da bindigun AK 47 sun kai hari makarantar gwamnati ta Ƙanƙara.

“An samu damar da jami’anmu suka fafata da yan bindigar a wata musayar wuta. Da yawa daga cikin daliban sun tsere daga makarantar. Don haka, safiyar yau DPO ya gano dalibai 200 sannan ya dawo dasu makarantar. Har yanzu muna kidaya domin gano ko yan bindigan sun yi nasarar garkuwa da kowasu dalibai.

“Tuni muka girke jami’an yan sanda a makarantar. Don haka, an yi musayar wuta tsakanin yan sanda da yan bindigan. Harma sun harbi wani jami’inmu wanda ya ji rauni sannan an kai shi asibiti kuma yana jin sauki."

A nata bangaren, jaridar HumAngle ta rahoto cewa daliban sun dawo ne bayan sun shafe tsawon dare a cikin wani jeji a safiyar yau Asabar, 12 ga watan Disamba.

HumAngle ta tattaro cewa mafi akasarin daliban da aka gano suna samun kulawar likitoci sakamakon samunsu da aka yi da raunuka daban-daban.

Yanzu Yanzu: Daruruwan daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare a Katsina sun dawo
Yanzu Yanzu: Daruruwan daliban da aka yi awon gaba da su a makarantar sakandare a Katsina sun dawo Hoto: @GovernorMasari
Source: Twitter

KU KARANTA KUMA: Halima Abubakar: Likita yar arewa da ke neman miji a shafin soshiyal midiya

Sai dai ta ce yawan daliban da ake tunanin an yi garkuwa da su ya dan ragu kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter.

Ga yadda ta wallafa a shafin nata:

“Da dumi-duminsa: Daruruwan dalibai daga makarantar Sanadare na gwamnatin Katsina sun dawo bayan sun shafe tsawon dare a jeji. Da dama daga cikin wadanda aka gano na samun kulawar likitoci na wasu raunuka daban-daban. Yawan wadanda ake zatton an yi garkuwa da su ya ragu zuwa wannan lokaci.”

Da farko mun ji cewa wasu 'yan bindiga sun yi awon gaba da dumbin dalibai daga wata makarantar sakandire ta kimiyya da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi jimamin mutuwar mawallafin jaridar Leadership Sam Nda-Isaiah

A cewar HumAngle, 'yan bindigar sun shiga har dakin kwanan daliban tare da yin awon gaba da su da duku-dukun safiyar yau, Asabar.

HumAngle ta wallafa cewa ana kidayar adadin daliban da aka sace a yayin da ta wallafa labarin da dumi-dumi a shafinta na sada zumunta; tuwita.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel