Fatai Aborode: An harbe wani jigon PDP har lahira a jihar Oyo

Fatai Aborode: An harbe wani jigon PDP har lahira a jihar Oyo

- An kashe wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Oyo

- An harbe jigon jam’iyyar, Fatai Aborode har lahira a gonarsa da ke karamar hukumar Ibarapa ta arewa

- Olugbenga Fadeyi, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda na jihar ya tabbatar da mutuwar Aborode

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe Fatai Aborode, wani jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Oyo.

An harbi jigon wanda ya sauya sheka zuwa PDP kwanan nan a gonarsa da ke hanyar Apodun, Igangan da ke karamar hukumar Ibarapa ta arewa a ranar Juma’a, 11 ga watan Disamba, jaridar The Cable ta ruwaito.

Olugbenga Fadeyi, kakakin yan sandan jihar Oyo da yake tabbatar da lamarin yace wasu yan bindiga hudu ne suka yi wa jigon fashi sannan suka harbe shi a yammacin ranar Juma’a.

Fatai Aborode: An harbe wani jigon PDP har lahira a jihar Oyo
Fatai Aborode: An harbe wani jigon PDP har lahira a jihar Oyo Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi jimamin mutuwar mawallafin jaridar Leadership Sam Nda-Isaiah

An kwashi marigayin wanda yayi takarar kujera a majalisar wakilai karkashin jam’iyyar Accord Party a 2015 zuwa asibitin Olugbon, Igboora inda aka tabbatar da mutuwarsa.

A cewar Fadeyi, an kai wa marigayin hari tare da manajansa a lokacin da suke komawa gida, inda yace a yanzu haka ana kokarin kama masu laifin.

A wani labarin, mun ji cewa daruruwan daliban da ake zatton wasu yan bindiga sun yi awon gaba da su daga wata makarantar sakandire ta kimiyya da ke karamar hukumar Kankara a jihar Katsina sun dawo.

KU KARANTA KUMA: Aminan Shugaba Buhari biyu da suka mutu bayan Abba Kyari

A cewar jaridar, daliban sun dawo ne bayan sun shafe tsawon dare a cikin wani jeji a safiyar yau Asabar, 12 ga watan Disamba.

HumAngle ta tattaro cewa mafi akasarin daliban da aka gano suna samun kulawar likitoci sakamakon samunsu da aka yi da raunuka daban-daban.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng