Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta shiga cikin jerin mutanen da suka fi tashe a intanet a 2020

Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta shiga cikin jerin mutanen da suka fi tashe a intanet a 2020

- Rahama Sadau ta yi nasarar shiga cikin jerin mutanen da suka fi tashe a yanar gizo a 2020

- Ko shakka babu jarumar ta Kannywood ta samu shiga wannan rukuni ne saboda rigimar da ta fada bayan bayyanar wasu hotunanta

- Ta kuma shiga jerin mutanen da aka fi neman karin haske a kansu a shafin Google a Najeriya a shekarar 2020

Shahararriyar jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa na Kannywood, Rahama Sadau, ta shiga sahun yan Najeriya da suka fi tashe a shafin yanar gizo cikin shekarar 2020.

Rahama ta kasance ta hudu a cikin wannan rukuni na mutanen da suka tashe a shafin na intanet a kasar, BBC Hausa ta ruwaito.

Har ila yau, Rahama ta shiga jerin mutanen da aka fi neman karin haske a kansu a shafin Google a shekarar 2020 a Najeriya, inda ta zo ta tara daga cikin mutane 10.

Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta shiga cikin jerin mutanen da suka fi tashe a intanet a 2020
Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta shiga cikin jerin mutanen da suka fi tashe a intanet a 2020 hoto: rahamasadau
Asali: Instagram

Bisa al’ada dama shafin Google kan fitar da kalmomi ko kuma sunayen da mutane suka fi lalubawa a shafin duk shekara a dukkanin kasashen duniya.

KU KARANTA KUMA: Manyan dalilai 6 da ke sa yan Najeriya barin kasarsu zuwa kasashen ketare

Bugu da kari kuma shafin kan yi wa sunayen rukuni ne, inda ake da rukunan mawaka da wakar kanta da wasanni da 'yan fim da fina-finan kansu da kuma tambayoyi.

Ba abun mamaki bane don Rahama ta shhiga wannan jeri duba ga abun day a faru da ita a watan Nuwamba na wannan shekara, inda aka samu cece-kuce tsakanin mutane a kanta bayan ta wallafa wasu hotuna dake nuna bayanta.

Lamarin hotunan nata ya kara ta’azzara ne bayan an samu wani mutum da yayi kalaman da bai dace ba kan Annabi Muhammadu a wajen sharhi da ke karkashin hoton nata.

KU KARANTA KUMA: Dokar majalisa: Shugaban kasa zai fuskanci barazanar tsigewa kan jinkiri wajen kafa majalisa

A wani labarin, Shekarar 2020 ta kasance cike da kalubale daban-daban, ba wai ga Najeriya ba kadai hatta ga duniya baki daya.

Annobar korona wacce ta fara a karshen shekarar 2019 ta yadu kamar gobarar daji a 2020 lamarin ya haifar da rikice-rikice na lafiya da tattalin arziki a duniya.

Korona ta haifar da dubban mace-mace a fadin duniya sannan ta durkusar da tattalin arzikin duniya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel