Dokar majalisa: Shugaban kasa zai fuskanci barazanar tsigewa kan jinkiri wajen kafa majalisa

Dokar majalisa: Shugaban kasa zai fuskanci barazanar tsigewa kan jinkiri wajen kafa majalisa

- Majalisar wakilai na neman gabatar da wani kudiri da zai tursasa zababben shugaban kasa ko gwamna bayyana yan majalisarsa cikin kwanaki 30 bayan karban mulki

- Sabuwar dokar na kuma neman majalisa ta tsige duk shugaban kasa ko gwamnan da ya gaza aikata hakan ba tare da kwakwaran dalili ba

- Mista Kpam Sokpo ne ya gabatar da wannan batu a zauren majalisar a ranar Laraba

Majalisar wakilai na neman sabon shugaban kasa ko gwamna ya kafa majalisarsa cikin kwanaki 30 bayan rantsar da shi ko ya fuskanci barazanar tsigewa daga majalisar dokokin tarayya ko na jiha, jaridar Punch ta ruwaito.

Dokar mika mulki da hawa kujerar mulki, 2020, Mista Kpam Sokpo ne ya gabatar da ita inda a cikinta ne wannan bukata yake, ya kuma gabatar da shi a majalisa ne a ranar Laraba.

Dokar ta kuma nemi a samar da kudade na musamman ga kwamitin mika mulki da kuma tursasa gwamnonin jiha sanar da yan majalisunsu a cikin wannan lokaci.

Dokar majalisa: Shugaban kasa zai fuskanci barazanar tsigewa kan jinkiri wajen kafa majalisa
Dokar majalisa: Shugaban kasa zai fuskanci barazanar tsigewa kan jinkiri wajen kafa majalisa Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: PDP ta lashe zaben da aka kammala a jihar Zamfara

Ya zo kamar haka:

“Bisa ga sassa na 147 da 302 na kundin tsarin mulki, da zaran shugaban kasa ya kama aiki, zai nada ministoci cikin kwanaki 30 daga ranar da ya karbi rantsuwar kama aiki.

“Shugaban kasar zai kafa tare da nada dukkanin gwamnatocin hukumomi da masana’antun da suka isa ayi nade nade cikin watanni biyu daga ranar da ya karbi mulki.

“A inda Shugaban kasar ya gaza ba dokokin hadin kai ba tare da kwakwaran dalili ba, toh za a kama shi da laifin saba ka’ida kamar yadda yake a karkashin sashi na 143(2) na kundin tsarin mulki.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Maina ya yanke jiki ya fadi a yayin shari’arsa a kotu

A wani labarin, a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba, 2020, majalisar FEC ta amince da bukatar batar da N59.35 wajen gyaran hanyoyi da aikin filin jirgin sama.

Jaridar Vanguard ta ce Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, ya gabatar da takardun kwangila na aikin N50.858bn da yake so a duba.

A zaman da aka yi jiya, FEC ta yi na’am da wannan bukata na gyaran titi a jihar Kano kuma aikin hanyar Kano zuwa Filato wanda za scu ci N50bn.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng