Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)

- Shekarar 2020 ta kasance cike da kalubale daban-daban, ba wai ga Najeriya ba kadai hatta ga duniya baki daya

- Annobar korona wacce ta fara a karshen shekarar 2019 ta yadu kamar gobarar daji a 2020

- Lamarin ya haifar da rikice-rikice na lafiya da tattalin arziki a duniya

Annobar korona ta haifar da dubban mace-mace a fadin duniya sannan ta durkusar da tattalin arzikin duniya.

A yayinda shekarar 2020 ke shirin karewa, Legit.ng ta duba wasu manyan yan siyasar da suka mutu a wannan shekara, mafi akasarinsu korona ce ta kashe su.

KU KARANTA KUMA: Wani ango mai fataucin miyagun kwayoyi ya shiga hannu wata daya kafin bikinsa

1. Abba Kyari

Abba Kyari, tsohon shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu sakamakon annobar COVID-19 a ranar Juma’a, 17 ga watan Afrilu.

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)
Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 Hoto: Bayo Omoboriowo
Asali: UGC

An tattaro cewa ya kamu da cutar korona a watan Maris bayan wani tafiya da yayi zuwa Jamus da Egypt.

An kwashi shugaban ma’aikatan zuwa jihar Lagas don jinya Jim kadan bayan sakamakon gwaji ya nuna yana dauke da cutar.

Ya nuna burin samun lafiya daga cutar, amma abun bakin ciki bai warke ba daga cutar.

2. Isiaka Abiola Ajimobi

Isiaka Abiola Ajimobi, tsohon gwamnan jihar Oyo, ya mutu a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuni, bayan fama da cutar COVID-19.

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)
Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 Hoto: @AAAjimobi
Asali: Twitter

An kwantar dashi a asibitin First Cardiologist and Cardiovascular Consultant Hospital, Lagas a ranar 2 ga watan Yuni, amma bai warke daga cutar ba.

Ya shaki numfashinsa na karshe yana da shekaru 70.

3. Sanata Adeboye Osinowo

Sanata Adeboye Osinowo ya mutu a ranar Litinin, 15 ga watan Yuni, yana da shekaru 64 a wani asitin Lagas.

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)
Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 Hoto: Sen Bayo Osinowo
Asali: Twitter

Har zuwa mutuwarsa, Osinowo na wakiltan yankin Lagas ta Gabas a majalisar dattawa karkashin APC.

4. Dr Wahab Adegbenro

Dr Wahab Adegbenro ya mutu sakamakon cutar COVID-19 a ranar Alhamis, 2 ga watan Yuni yana da shekaru 65.

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)
Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 Hoto: The Sun
Asali: UGC

Har zuwa mutuwarsa, ya kasance Kwamishinan lafiya na jihar Ondo.

5. Philip Shekwor

Philip Shekwo ya kasance Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Nasarawa har zuwa mutuwarsa.

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)
Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

An tsinci gawarsa a ranar 22 ga watan Nuwamba, yan sa’o’i kadan bayan an yi garkuwa da shi a gidansa.

6. Mallam Ismaila Isa Funtua

Mallam Ismaila Isa Funtua ya rasu sakamakon bugun zuciya a ranar Litinin, 20 ga watan Yuli.

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)
Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 Hoto: @aishambuhari
Asali: Twitter

Ya kasance makusancin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

7. Tunde Braimoh

Har zuwa mutuwarsa, Tunde Braimoh ya kasance dan majalisar jihar Lagas. Ya mutu a ranar Juma’a, 10 ga watan Yuli.

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)
Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 Hoto: @TundeBraimoh1
Asali: Twitter

Dan majalisar ya mutu yan makonni kafin bikin cikarsa shekaru 60 a duniya.

KU KARANTA KUMA: Yajin aiki: Gwamnatin tarayya ta ɗage zamanta da kungiyar ASUU

8. Sanata Buruji Kashamu

Shahararren dan siyasan na Najeriya kuma jigon PDP, Sanata Buruji Kashamu ya mutu sakamakon cutar Coronavirus.

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)
Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 Hoto: @benmurraybruce
Asali: Twitter

Sanata Ben Murray-Bruce ne ya sanar da mutuwarsa a yammacin ranar Asabar, 8 ga watan Agusta.

9. Sanata Rose Okoji Oko

Rose Okoji Oko, ta kasance sanata mai wakiltan yankin arewacin Cross River a karkashin jam’iyyar PDP. Ta mutu a cibiyar lafiya a UK.

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)
Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 Hoto: @EthelbertMgbado
Asali: Twitter

10. Hajia Zuwaira Hassan

Hajia Zuwaira Hassan, tsohuwar kwamishinar lafiya ta jihar Bauchi ta mutu a wani mummunan hatsarin mota.

Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 (jerin sunaye)
Kyari da manyan yan siyasa 9 da suka mutu a 2020 Hoto: @Bauchitrends
Asali: Twitter

Ta mutu a safiyar ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamba a kauyen Zaranda, kimanin kilomita 36 daga garin Bauchi.

A wani labarin, Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa fiye da mutum dubu talatin da takwas sun nuna sha'awar son zama 'yan Nigeria.

Dakta Shuaib Begore, babban sakatare a ma'aikatar harkokin cikin gida, ya sanar da hakan a Abuja.

Matasa daga Nigeria kan saka rayuwarsu cikin hatsari domin samun damar tsallakawa zuwa kasashen duniya musamman turai.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng