Manyan dalilai 6 da ke sa yan Najeriya barin kasarsu zuwa kasashen ketare

Manyan dalilai 6 da ke sa yan Najeriya barin kasarsu zuwa kasashen ketare

- A baya-bayan nan yan Najeriya na ta tafiya wajen kasar don yin wasu harkoki

- Wadanda ke da kudi sun garzaya abunsu Amurka, Turai da kasashen Asia

- A yanzu haka, wasu da dama na gwagwarmayar ganin sun bar kasar

1. Hanyar shigowar kudi

Yan Najeriya na sane da cewar lokaci da karfin da suke zubawa wajen aiki a kasar zai samar masu da karin kudaden shiga idan suka yi amfani da shi a kasar waje.

Kasancewa mai kwazo a kasar waje yana nufin samun karin kudade a asusun bankin mutum, amma bah aka lamarin yake ba a gida Najeriya.

2. Damar samun ayyukan yi

Akwai damammaki na samun aikin yi a kasar waje fiye da yadda mutum zai samu a Najeriya. Mutanen da ke tururuwan fita daga kasar na sane da wannan.

Lamarin rashin aikin yi a Najeriya ya ta’azzara sannan matasan Najeriya da dama sun kaji da neman ayyukan da babu su.

Sun san cewa akwai wadannan ayyukan shiyasa suke barin kasar da zaran sun samu dama domin samawa kansu damammaki a kasashen waje.

Kwanaki Legit.ng ta rahoto yadda wata budurwa mai suna Mfon Abia ta samu aikin da bata nema ba a kasar Amurka.

Ta ce ta samu kira daga The Academy, Miami, Florida, inda suka bata aiki da neman ta tura takardunta idan tana da ra’ayin aikin.

Ta wallafa a shafinta na Linkedln:

“Ina farin cikin sanar da wannan majalisa mai karamci cewa a ranar Litinin, 3 ga watan Agusta 2020, zan tashi daga yar Najeriya mara aikin yi sannan zan fara aiki a The Academy, Miami, Florida, USA.”

Manyan dalilai 6 da ke sa yan Najeriya barin kasarsu zuwa kasashen ketare
Manyan dalilai 6 da ke sa yan Najeriya barin kasarsu zuwa kasashen ketare Hoto: Nairametrics
Source: UGC

3. Ilimi

Ingancin ilimi a Amurka da Turai ya fi wanda muke da shi a Najeriya, wannan ne daya daga cikin dalilan da yasa yan Najeriya ke barin wannan kasar.

Da kwalin karatun digiri da mutum zai samu a kasar waje, suna sane da cewar kamfanoni a Najeriya za su dunga rububin daukarsu aiki.

4. Cimma burin rayuwa

Mutane da damamna samun damar cika burin rayuwarsu a kasar waje cikin sauki fiye da yadda za su samu a Najeriya.

Wadanda ke da fasaha sun fi samun karbuwa a kasashen waje fiye da yadda suke samu a Najeriya.

Burin kowa shine ya samu ci gaba a duk bangaren da ya samu kansa, kuma wannan ne dalilin da yasa mutane suke barin Najeriya idan suka tabbatar da cewar za su cimma muradinsu cikin sauki a waje.

5. Kiwon lafiya

Mutane da daman a fita wajen kasar saboda samun tsarin kiwon lafiya mai inganci da ke kasar waje. Mutane sun gwammaci su tayar da iyalansu a kasar da ke ba fannin lafiyarta muhimmanci sosai.

6. Sama wa yayansu takardar yan kasa a wasu kasashe

Wannan ya kasance daya daga cikin dalilan da ke sa yan Najeriya barin kasar. Suna so yaransu su samu takardan yan kasa biyu da kuma samun damammaki da kowani da a kasar waje zai samu.

A wani labarin, gwamnatin tarayya ta nada Abubakar Fikpo a matsayin mukaddashin darakta janar na hukumar daukan ma’aikata, domin ya maye gurbin Dr Nasiru Argungu wanda aka dakatar daga matsayin a ranar 7 ga watan Disamba.

Festus Keyamo, karamin ministan kwadago da aikin yi, ya tabbatar da nadin a wata wasika mai taken “nada ka a matsayin mukaddashin darakta janar na hukumar daukan ma’aikata."

An kuma aika wasikar zuwa ga Fikpo a ranar Laraba, 9 ga watan Disamba, a Abuja, jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel