Farfesa Ignatius Uduk ya na zaman gidan gyaran hali a jihar Akwa Ibom

Farfesa Ignatius Uduk ya na zaman gidan gyaran hali a jihar Akwa Ibom

- Ignatius Uduk zai shafe akalla kwanaki biyar a gidan yari kafin ya samu beli

- Farfesan ya na kotu da hukumar EFCC ne bisa zargin hannu a magudin zabe

- Malamin makarantar ya karyata zargin da ake yi masa na murde zaben 2019

A ranar Laraba ne Alkalin babban kotun tarayya da ke garin Uyo, Akwa Ibom, ya bukaci a tsare Farfesa Ignatius Uduk a gidan gyaran hali.

Premium Times ta fitar da rahoto a ranar 9 ga watan Disamba, 2020, cewa Ignatius Uduk zai yi kwanaki biyar a tsare kafin ya iya samun beli.

Jaridar ta ce malamin makarantar zai san ko zai samu beli a ranar Litinin, 14 ga watan Disamba. Kafin nan za a cigaba da tsare sa a kurkukun.

Hukumar zabe na kasa watau INEC, tana zargin Ignatius Uduk wanda ke koyar wa a jami’ar Uyo, Akwa Ibom da laifuffuka uku a gaban kotu.

KU KARANTA: Maina ya yanke jikiya fadi a kotu

Uduk ya musanya cewa ya aikata laifuffukan da ake tuhumarsa da su. Farfesan ya kuma bukaci a ba shi beli ta hannun lauyansa, Samuel Ndah.

Barista Samuel Ndah ya na neman beli ne ta sanayya, amma Lauyan da ya tsayawa hukumar INEC ya roki Alkali ya guji sakin Farfesa Uduk.

Lauyan da ya shigar da kara a madadin hukumar da ke gudanar da zabe a Najeriya ya ce bai dace a kyale Uduk ba, ya roki a cigaba da tsare shi.

Dalilin da INEC ta kafa shi ne Farfesan bai zo kotu ba har sai da ya ji an yi cigiya, za a kama shi.

Farfesa Ignatius Uduk ya na zaman gidan gyaran hali a jihar Akwa Ibom
Farfesa Ignatius Uduk Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

KU KARANTA: Za mu garkame Jami’o’in kasuwan fadin kasar nan - Kungiyar Dalibai

Alkali mai shari’a A.E Archibong bai bada umarnin a saki malamin zaben ba, hakan ya na nufin zai cigaba da zaman gidan kaso har makon gobe.

A kasar waje kun ji cewa shugaba Donald Trump ya gagara samun nasarar zabe a babban kotun Amurka, inda ya ke kalubalantar nasarar Joe Biden.

Alkalin Kotun koli ya tabbatar da nasarar Joe Biden da jam'iyyar adawa ta Democrat a Pennsylvania, ya ce babu bukatar a sake bibiyar kuri'u.

Mike Kelly ya roki Kotu ta haramta amfani da kuri’un E-mail da aka yi a jihar Pennsylvania.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel