Bidiyon yadda Maina ya yanke jiki ya fadi a kotu

Bidiyon yadda Maina ya yanke jiki ya fadi a kotu

- A ranar Alhamis ne aka sake gurfanar da tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina, a gaban kotu

- Yayin zaman kotu na ranar Laraba, Maina ya ce bai aikata laifin komai ba duk da cewa hukumar EFCC ta na yi masa tuhuma 12 a gaban kotu

- Kafin sake gurfanar da shi a gaban kotun ranar Laraba, Maina ya tsallake beli, ya sulale zuwa jamhuriyar Nijar

An kwashi dirama da 'yan kallo a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja yayin da Abdulrasheed Maina ya yanke jiki ya fadi bayan gurfanarsa a ranar Alhamis.

A wani lokaci can a baya, Maina ya taba yanke jiki ya fadi a harabar kotu, lamarin da yasa ya koma zuwa kotun a kan keken guragu, kamar yadda TheCable ta wallafa.

Sai dai, bayan an bayar da shi beli, Maina ya mike, ya sulale, ya gudu ya bar Nigeria kamar yadda ya taba yi a baya.

Maina, tsohon shugaban hukumar fansho (PRTT), ya shaidawa babbar kotun tarayya a Abuja cewa babu wata tuhuma da zai amsa akan zarge-zargen da Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta ke yi masa.

KARANTA: A villa ake iskanci na gaske kuma Buhari ne jagora; Aisha ta mayar da martani a kan gargadin shugaba Buhari

Bidiyon yadda Maina ya yanke jiki ya fadi a kotu
Bidiyon yadda Maina ya yanke jiki ya fadi a kotu
Source: Twitter

Maina ne ya faɗawa babban alƙalin kotun, Okon Abang, hakan jim kaɗan bayan EFCC ta rufe shari'ar, ta bakin lauyanta, Farouk Abdullahi, a ranar Laraba.

Ya ce kundinsa da kimarsa zasu kasance ba tare da kowanne irin tabo ba nan ba da jimawa ba domin gaskiya za ta bayyana.

KARANTA: Gwamnatin tarayya ta na amfani fasahar Isra'ila wajen leken asirin wayoyin 'yan Nigeria

Duk da cewar ana tuhumarsa da laifuka 12 da suka shafi almundahanar kuɗaɗe da suka kai kimanin Naira biliyan ₦2b, Maina ya yi iƙirarin cewa bai aikita ko ɗaya cikin laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa ba.

An dawo da Maina ga hukumomin Najeriya bayan kama shi a jamhuriyyar Nijar a ranar Litinin.

Ya tsallake beli wanda ya kai ga kama Sanata mai ci, Ali Ndume, wanda ya tsaya masa a kotun kafin a bayar da shi beli.

Legit.ng Hausa ta rawaito cewa jami'an binciken sirri da hadin gwuiwar na hukumar yaki da cin hanci sun kama Abdulrasheed Maina a Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba.

Kamfanin dillancin labarai na PRNigeria ya ce an kama Maina a wani gari da ke cikin Jamhuriyar Nijar.

A cewar majiyar jaridar, an samu nasarar kama Maina ne saboda kyakyawar alakar da ke tsakanin jami'an tsaron Najeriya da Nijar.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel