Jerin ‘Yan wasan kwallon da suka dawo suka rasa dukiyarsu shekaru da yin ritaya

Jerin ‘Yan wasan kwallon da suka dawo suka rasa dukiyarsu shekaru da yin ritaya

- Akwai wasu tsofaffin ‘Yan wasan kwallon da suka tsiyace bayan sun ajiye wasa

- Daga cikin wadanda ritaya ta sa suka tsiyace har da Marigayi Diego Maradona

- Babayaro, Ronaldinho da Royson Drenthe suna cikin sauran da fatara ta kama su

Legit.ng ta tattaro maku jerin wasu ‘yan wasan kwallon kafa 12 da su kawo ba su da komai a Duniya, bayan sunyi ritaya daga taka leda.

Tsohon ‘dan wasan Super Eagles Celestine Babayaro bayan ya buga wa Chelsea da Newcastle United na Ingila, ya tsiyace a shekarar 2011.

Wani ‘dan kwallon da yanzu bai da arziki shi ne Royson Drenthe wanda ya buga wa manyan kungiyoyin kwallon kafa har da Real Madrid.

Ronaldinho wanda ya taba zama gwarzon Duniya shi ne ya fi ba kowa mamaki a jerin, an yi lokacin da $7 kadai aka samu a bankinsa gaba da baya.

KU KARANTA: Ronaldinho ya yi kwanan gidan yari Paraguay

Marigayi Diego Maradona shi ma ya samu kansa a irin wannan mawuyacin hali a shekarar 2009.

1. Diego Maradona (kasar Argentina) – ya tsiyace a 2009.

2. Ronaldinho (Brazil) – £5 rak ke cikin asusun bankinsa a 2020

3. Royston Drenthe (Holland) – bai da komai a 2020.

4. David James (Ingila) – ya tsiyace a 2015.

5. Asamoah Gyan (Ghana) – £600 suka rage a asusun bankinsa a 2018.

6. Paul Gascoigne (Ingila) – Ana zargin bai da ragowar komai a banki.

7. Celestine Babayaro (Najeriya) – ya tsiyace a 2011.

8. John Arne Riise (Norway) – ya tsiyace tun 2007.

KU KARANTA: Kwayoyi suka kashe Maradona

Jerin ‘Yan wasan kwallon da suka dawo suka rasa dukiyarsu shekaru da yin ritaya
Ronaldo de Assis Moreira 'Gaucho' Hoto: bbc.co.uk
Source: UGC

9. Brad Friedel (Amurka) – ya ce ya tsiyace a 2011.

10. Keith Gillespie (A/Ireland) – ya tsiyace a 2010.

11. Eric Djemba Djemba (Kamaru) – ya tsiyace a 2007.

12. Willem Vries (Afrika ta Kudu) – Bai da kudin da zai saye akwatin talabijin.

A 2017 ne ku ka ji cewa Ronaldinho ya yi bankwana da tamola. 'Dan wasan ya shaida wa jaridar Marca ta kasar Sifen wannen ne bayan ya yanke hukuncin.

Ronaldinho mai shekaru 40 a duniya yayi aiki a matsayin jakada a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, inda ya yi tashe kafin ya tafi AC Milan a Italiya.

Bayan ritayar Ronaldinho ne aka kama fitaccen tsohon ‘Dan wasan Duniyan da fasfon bogi.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel