Ronaldinho ya yi sallama da tamola
Sana'ar taka leda ta fitaccen dan kwallon kafar nan, Ronaldinho, tazo karshe kamar yadda dan uwansa kuma wakilinsa, Assis ya bayyanawa manema labarai na jaridar Marca ta kasar Andalus.
A halin yanzu, Ronaldinho mai shekaru 37 a duniya yana aiki ne a matsayin jakada a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, inda a wata ganawa da manema labarai ya bayyana cewa girma ya kama shi ta yadda ba zai motsi ba filin daga.
Ya ci gaba da cewa, wannan lamari ya sanya ya ga ya kamata ya tattara ina-sa-ina-sa domin yin sallama da sana'ar taka leda.
Assis ya bayyana cewa, babu wani wasan kwallon kafa na bankwana da aka shirya domin sadaukarwa ga shahararren dan kwallon, sai dai akwai yiwuwar aiwatar da hakan bayan an kammala kwallon gasar kofin duniya.
KARANTA KUMA: Gwamnonin APC sun gujewa taron shugabannin jam'iyya
Legit.ng ta fahimci cewa, kungiyar kwallon kafa ta Fluminense ita ce kungiya ta karshe da Ronaldinho ya baiwa gudunmuwarsa, inda tarihi ya bayyana cewa dan kwallon ya wakilci wasu kungiyoyin kwallon kafa da suka hadar da, Gremio, PSG, Barcelona, Milan, Flaminengo, Atletico Mineiro da kuma Queretaro.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng