Alkali ya bukaci a cigaba da tsare Ronaldinho a gidan yarin Paraguay

Alkali ya bukaci a cigaba da tsare Ronaldinho a gidan yarin Paraguay

Shararren tsohon ‘Dan wasan Duniyan nan, Ronaldinho ya na ganin ta kansa bayan da Alkali ya bada umarnin cewa a cigaba da tsare shi a gidan kaso a kasar Paraguay.

Ana zargin Ronaldinho da amfani da takardun shiga kasar waje watau fasfo na bogi. Ronaldinho ya yi ikirarin cewa bai da masaniyar takardun da ya ke rike da su na jabu ne.

Tsohon ‘dan kwallon na kasar Brazil ya fadawa kotu cewa sam bai lura ya na rike da takardun bogi ba. Lauyan Tauraron ya yi kaca-kaca da shi a dalilin wannan katabora.

Jami’an kasar Paraguay sun yi ram da Ronaldinho ne tare da wani ‘Danuwansa, Roberto, a wani otel mai suna Sheraton, a karshe aka gurfanar da su tare gaba daya a kotu.

Akwai yiwuwar a daure Ronaldinho da ‘Danuwan na sa na tsawon rabin shekara idan aka same su da laifi. Sai dai wani Lauyan da ke karesu ya yi tir da matakin da kotu ta dauka.

KU KARANTA: Rahotanni: 'Yan Sanda sun kama Ronaldinho a kasar Paraguay

Alkali ya bukaci a cigaba da tsare Ronaldinho a gidan yarin Paraguay
Tauraro Ronaldinho a hannun 'Yan Sanda a kasar Paraguay
Source: Instagram

Wannan Lauya ya bayyana cewa Jakadun kasar Brazil sun shiga cikin maganar domin ganin an fito da Ronaldinho wanda ya bugawa kasarsa kwallon kafa na shekara da shekarau.

Kwanakin baya an karbe fasfon Ronaldinho bayan an kama shi da laifin su a yankin da bai halatta ba. Wannan ba shi ba ne karon farko da Tauraron ya samu kansa da hukuma.

Ronaldinho ya shafe daren Juma’a ne a ragar ‘Yan Sanda tare da ‘Danuwansa Roberto Assis. Lauyan da ke karesu, ya roki a rika tsare su daga dakunansu, amma Alkalin kotu ya ki.

Wadannan Bayin Allah da su ka shigo Kasar Paraguay a makon jiya sun fadawa kotu cewa su na fama da ciwon zuciya, amma Alkali ya nuna cewa babu wata hujja da ta nuna hakan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel