‘Yan Sandan Argentina na gabatar da bincike a kan abin da ya kashe Maradona

‘Yan Sandan Argentina na gabatar da bincike a kan abin da ya kashe Maradona

- Ana bincike game da abin da ya kashe Diego Maradona ya na shekara 60

- An gano cewa tsohon ‘dan kwallon ya na yawan shan magunguna rututu

- Akwai yiwuwar wadannan kwayoyi su ka karasa kashe Tauraron Duniyan

Diego Maradona ya kasance yana kan magunguna samfurin ‘Antidepressants da Antipsychotics’ dake kashe masa bakin-ciki, juyayi da damuwa.

Rahotanni daga The Nation sun bayyana cewa tsohon wasan kwallon kafan ya na amfani da wadannan magunguna ne wajen maganin ciwonsa.

Ana samun wannan labari ne bayan ‘yan sandan kasar Argentina sun tsefe kaf gidan likitan tsohon ‘dan wasan, suna binciken abin da ya kashe shi.

Jaridar tace jami’an tsaro suna zargin cewa akwai hannun likitan a mutuwar wannan Bawan Allah.

KU KARANTA: Yadda Maradona ya taimaka wa Messi a rayuwa

Abin da malaman lafiya su ka fada shi ne Diego Maradona ya mutu ne a dalilin bugawar zuciya wanda abin har ya kai ruwa ya cika masa huhu.

Masana lafiya suna ganin cewa magugunan da Maradona ya rika sha ne su kayi sanadiyyar jefa zuciyarsa cikin matsala, abin da ya kai ga ajali.

‘Yan sanda sun shiga ofis da gidan likitan marigayin, Leopoldo Luque, bayan iyalin Maradona (Dalma da Giannina) sun ba jami’an tsaro wasu bayanai.

Kwayoyin da Maradona yake sha sun hada da Quetiapine mai maganin takaici da damuwa, sai kwayar Gabapentin mai maganiin ciwon jijiyoyi.

KU KARANTA: Lokutan da tsohon Tauraron kwallon kafa Maradona ya kafa tarihi

‘Yan Sandan Argentina na gabatar da bincike a kan abin da ya kashe Maradona
Marigayi Maradona Hoto: GettyImages
Asali: Getty Images

Likitoci sun kuma gano cewa kafin tsohon ‘dan kwallon ya mutu, zuciyarsa ta daina kai jini yadda ya kamata zuwa sauran bangarorin jikinsa.

Maradona ya kan sha irinsu Naltrexone, Venlafaxine, Lurasidone, Omeprazol, da Vitamin B complex.

Yau mako guda kenan da ku ka ji cewa Diego Maradona ya mutu. Tsohon 'dan wasan ya rasu yana da shekaru 60 bayan ya yi ta fama da rashin lafiya.

A baya bayan nan ne aka sallamo Diego Maradona daga asibiti bayan yi masa aiki a kwakwalwa, sakamakon gano cewa akwai gudan jini a kwakwalwarsa.

Fitaccen dan wasan ya rasu a ranar Laraba 25 ga watan Nuwamban shekarar 2020 a gida.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng