NSCDC ta ceto wata mata da yan uwanta suka kulle ta tsawon watanni 5 a daki

NSCDC ta ceto wata mata da yan uwanta suka kulle ta tsawon watanni 5 a daki

- An yi nasarar ceto wata mata wacce ’yan uwanta suka kulle a wani daki tsawon wata biyar

- Matar da aka ceto mai suna Saratu Ayuba tana zaune ne a unguwar Bolari da ke garin Gombe

- An rufe matar ne bisa zarginta da ake yi da yin cikin shege tare da haifewa

A karshen mako ne rundunaar tsaro ta NSCDC a jihar Gombe ta ceto wata mata yar shekara 35 wacce ake zargin yan uwanta sun kulle ta tsawon fiye da wata biyar.

An ceto Saratu Ayuba da ke zama a kwatas din Bolari a birnin Gombe sakamakon wasu bayanai da aka samu daga makwabta, bayan sun gano halin da take ciki na azabtuwa.

Wasu yayyenta maza ne suka rufe ta a daki tsawon sama da watanni biyar, bayan zargin cewa ta yi cikin shege da kuma haifewa, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

NSCDC ta ceto wata mata da yan uwanta suka kulle ta tsawon watanni 5 a daki
NSCDC ta ceto wata mata da yan uwanta suka kulle ta tsawon watanni 5 a daki Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Shaidu sun bayyana cewa an daure Saratu da mari tare da jaririyar da ta haifa yar watanni biyu a cikin wani daki mara tsafta, a gidansu da ke Bolari.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An dawo da zanga zangar #EndSARS a garin Osogbo

Saratu, wacce ta tsinci kanta a cikin wani yanayi mara kyan gani ba tare da suturar kirki ba, ta ce shayi da biredi kawai ake bata sau daya a rana tsawon watanni biyar da tayi a kulle.

Saboda yanayin da take ciki na rashin samun kula, ta ce bata samar da wadataccen ruwan nono domin shayar da jaririyarta.

Ta bayyana cewa tsohon mijinta ne yayi mata ciki, inda ta kara da cewa da gangan yayi hakan domin tursasa yayyenta mayar da ita gidansa. Ta ce tsohon mijin nata yayi mata saki biyu bisa kuskure.

Ta kara da cewa tana da ’ya’ya biyu a aurenta na farko; Alkasim mai shekaru 10 da kuma Fatima shekara takwas.

Sai dai kuma, yayan Saratu mai suna Muhammad Tajuddin ya ce sun kulle ta ne bayan likitoci sun gano tana da tabin hankali.

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole PDP ta karbi kayen da ta sha cikin mutunci, In ji Gwamna Bala Mohammed

A wani labarin, wata matashiyar budurwa mai shafin Twitter @3yesharu ta yi kira ga mazan Hausawa magidanta a kan su duba yiwuwar yin karin aure, cewa yan mata da ke kan layi sun gaji da jira.

Matashiyar wacce ta fito daga yankin arewacin kasar ta yi kiran ne ga mazan Hausawa da suka yi aure fiye da shekaru biyar da suka gabata.

Ta wallafa a shafinta na Twitter: “Mazan arewa da suka yi aure tsawon shekaru 5+ ina ganin lokaci yayi da za ku fara kallonmu yan rukunin B. Mun isa a kwashemu amma layin baya tafiya.”

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng