Yanzu Yanzu: An dawo da zanga zangar #EndSARS a garin Osogbo
- Matasa sun fara gudanar da sabuwar zanga zangar EndSARS a garin Osogbo, jihar Osun
- Sun gudanar da gangamin ne a yau Litinin, 7 ga watan Oktoba inda suka yi tattaki har zuwa majalisar dokokin jihar
- Masu zanga zangar da ke kira ga shugabanci nagari da wasu bukatun sun nemi zantawa da shugabannin majalisar
Wasu matasa karkashin inuwar gangamin #EndSARS, a ranar Litinin, 7 ga watan Disamba, sun gudanar da zanga zangar a Osogbo, babbar birnin jihar Osun.
Sun yi gangamin ta cikin unguwannin Osogbo zuwa majalisar dokokin jihar Osun, inda suka bukaci tattaunawa da shugabannin majalisar, jaridar Punch ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Mazan Hausawa su rinƙa auren mata fiye da 1, budurwa ta koka da rashin samari
Zanga zangar wanda Emmanuel Adebisi ya jagoranta na kira ga shugabanci nagari da sauran abubuwa.
A wani labarin, mun ji cewa biyo bayan tsoro da ake yi na barkewar sabuwar zanga-zangar EndSARS, an tura jami’an yan sanda da na sojoji zuwa mashigin harabar Lekki Toll Gate.
Masu ababen hawa da masu tafiya a kafa sun sanar da manema labarai cewa an zuba jami’an tsaro a wajen a safiyar ranar Litinin, 7 ga watan Disamba.
KU KARANTA KUMA: Ya zama dole PDP ta karbi kayen da ta sha cikin mutunci, In ji Gwamna Bala Mohammed
Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda, Muyiwa Adejobi, ya ki amsa kiran wayar da aka yi masa a safiyar yau Litinin.
A wani lamarin kuma, wamnan jihar Legas, Babajide Sanwoolu, a ranar Alhamis ya bada milyan goma ga kowanne cikin matan jami'an yan sanda shida da aka kashe yayin zanga--zangan EndSARS.
Gwamnan ya yi hakan ne domin cika alkawarin da yayi lokacin ganawarsa da yan sandan jihar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng