Ya zama dole PDP ta karbi kayen da ta sha cikin mutunci, In ji Gwamna Bala Mohammed
- Gwamnan jihar Bauchi ya magantu bayan kayen da jam'iyyarsa ta PDP ta sha a zaben cike gurbi
- Bala Mohammed ya shawarci mabiya jam'iyyar a kan su karbi sakamakon cikin mutunci domin shine nufin Allah
- Ya kuma yi kira garesu a kan kada su bari hakan ya raba kansu ko kuma a dunga ganin laifin juna
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi ya bukaci mambobi da magoya bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da su amshi kayen da suka sha a zaben cike gurbi na majalisar dokokin jihar da aka kammala cikin mutunci.
Gwamnan wanda ya bayyana kayen a matsayin nufin Allah ya karfafawa masu biyayya ga jam’iyyar a kan kada su bari wannan lamari na wucin-gadi ya raba kansu.
Gwamna Bala Mohammed yayinda yake bayyana kayen a matsayin darasi ga kowa, ya bayyana cewa a matsayinsu na jarumai, ya zama dole gwamnatinsa da PDP su shirya yadda za su dawo da kayen da suka sha cikin mutunci, dabaru da kuma aiki tare.
KU KARANTA KUMA: Gwamnan Nasarawa ya ziyarci Borno, ya je da muhimmiyar bukata 1
“Dukkan godiya sun tabbatar ga Allah. Kayen da jam’iyyarmu ta sha darasi ne garemu dukka, amma babu wanda za a daura wa laifi.
“Ku tuna mun rasa kujeru 21 na majalisar dokokin jiha da kujeru uku na majalisar dattawa a 2019 amma Allah ya bamu nasara a zaben gwamna. Kada mu yi wasa da lamarin ta hanyar ganin laifin juna, rikicin cikin gida, zarge-zarge da kuma rashin yarda,” ya bayyana a ranar Lahadi.
Ya kuma yaba ma dukkanin mambobin PDP kan goyon bayansu da gudunmawarsu wajen tabbatar da nasarar gwamnatinsa, Channels Television ta ruwaito.
A gefe guda, jam'iyyar APC ta kara samun tabbacin cewa har yanzu 'yan Najeriya ita suke yayi, bayan ganin dumbin nasarorin da ta samu a zaben maye gurbi da aka yi, kamar yadda fadar shugaban kasa tace.
Malam Garba Shehu, babban hadimin shugaba Muhammadu Buhari a kan harkar yada labarai ya sanar da hakan.
KU KARANTA KUMA: Seriake Dickson zai wakilci Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya doke APC
A wata takarda da ya saki a Abuja ranar Lahadi, 6 ga watan Disamba, kakakin shugaban kasa yace hakika Shugaba Muhammadu Buhari ya yi matukar farinciki da jin nasarorin da APC ta samu a zaben maye gurbin da aka yi.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng