Mazan Hausawa su rinƙa auren mata fiye da 1, budurwa ta koka da rashin samari

Mazan Hausawa su rinƙa auren mata fiye da 1, budurwa ta koka da rashin samari

- Wata matashiyar budurwa daga arewa ta gaji da zaman gwauranci don haka ta je shafin soshiyal midiya don yin magana

- Budurwa mai shafin Twitter @3yesharu ta yi kira ga mazan Hausawa da suka yi aure fiye da shekaru biyar a kan su duba yiwuwar karin aure

- A cewarta, layin yan matan da ke jira a dauke su a matsayin matan aure na biyu ya dade da cika

Wata matashiyar budurwa mai shafin Twitter @3yesharu ta yi kira ga mazan Hausawa magidanta a kan su duba yiwuwar yin karin aure, cewa yan mata da ke kan layi sun gaji da jira.

Matashiyar wacce ta fito daga yankin arewacin kasar ta yi kiran ne ga mazan Hausawa da suka yi aure fiye da shekaru biyar da suka gabata.

Ta wallafa a shafinta na Twitter:

“Mazan arewa da suka yi aure tsawon shekaru 5+ ina ganin lokaci yayi da za ku fara kallonmu yan rukunin B. Mun isa a kwashemu amma layin baya tafiya.”

Mazan Hausawa su rinƙa auren mata fiye da 2, budurwa ta koka da rashin samari
Mazan Hausawa su rinƙa auren mata fiye da 2, budurwa ta koka da rashin samari Hoto: @yesharu/Twitter, Shacara
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Zanga zangar EndSARS karo na 2: Sojoji da ƴan sanda sun mamaye babbar ƙofar Lekki

Yan Najeriya sun je bangaren yin sharhi a karkashin rubutunta don bayyana ra’ayinsu.

Shafin @mbkusharki ta wallafa:

“Abun bakin ciki rukunin A sun daga ginshiki mai inganci ta yadda yiwuwar shigowar rukunin B na a kusa da 0%.”

@olahassan ya rubuta:

"Dole sai mazan Arewa? Wasun mu daga kudu maso yamma mun fi dacewa. Ki tambayi kawayenki da suka yi aure daga wannan yanki na Naija yadda muke da dadin zama.”

@deendeenoo ta wallafa:

"Wallahi kin fadi zukatan yan mata da dama. Amma soshiyal midiya ya sauya tunanin maza a yanzu saboda wasu mata da dama suna kokarin yin rayuwa sabanin wanda addini da al’ada suka koyar dasu. Maza na gudun mata masu aikata hakan.”

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole PDP ta karbi kayen da ta sha cikin mutunci, In ji Gwamna Bala Mohammed

@mustaphahodio ya rubuta:

“Da sai ki yi kira ga yan uwanki mata a Batch A don su barmu mu kwashi yan Batch B.”

A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika wata tawaga karkashin jagorancin ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya, zuwa wajen bikin yarinyar babban dogarinsa, Amina Idris Ahmed da angonta, Hayatuddeen Mustapha Abba.

Shugaba Buhari, a sakonsa, ya shawarci sabbin ma’auratan a kan su gina ginshikin aurensu bisa yarda da mutunta juna.

Shugaban kasar, a cikin wata sanarwa da kakinsa, Garba Shehu ya saki, ya bukaci ma’auratan da “kowanne ya kula da dan uwansa kamar yadda yake so a kula da shi” sannan ya yi masu fatan nasara a gidan aurensu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng