2023: Kungiyar arewa ta fara neman magajin Buhari

2023: Kungiyar arewa ta fara neman magajin Buhari

- An fara tsere kan wanda zai gaji Shugaban kasa Muhammadu Buhari a kasar

- Wata kungiyar Arewa ta kaddamar da neman sahihin dan takara da zai zama shugaban kasa a 2023

- Kungiyar ta kuma bude idonta a kan talauci da rashin tsaro da ke yi wa yankin arewacin Najeriya barazana

Yayinda aka mayar da hankali kan tattauna batun wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari, wata kungiya ta kafa kwamiti domin fara neman sabon shugaban kasa.

Kungiyar arewa, Progressives Movement for Democracy (PDM), ta bayyana hakan a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, cewa an ba kwamitin damar samo sahihin dan takara wanda arewa ke gabansa, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Da yake magana a yayin rantsar da kwamitin, shugaban kungiyar, Muhammad Auwal Musa, ya ce arewa ta gaji da zama cibiyar talauci da rashin tsaro a kasar.

2023: Kungiyar arewa ta fara neman magajin Buhari
2023: Kungiyar arewa ta fara neman magajin Buhari Hoto: Bashir Ahmed
Asali: Facebook

A cewarsa, manufar kungiyar shine hada kan yan arewa domin ci gaban yankin.

KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP na shirin tarwatsewa yayinda karin wasu gwamnoni ke barazanar komawa APC

“Muna son hadin kai domin neman muradin arewa gabannin zabukan 2023, kamar yadda muka yi a 2014 lokacin da aka kafa APC.

“Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar kujerar a matsayin shugaba a 2023. Mun yanke shawarar hada kai da kuma hada yan arewa a karkashin inuwa guda domin mu kawo ci gabanmu hadewarmu a siyasa.

“Dole sai mun yi aiki da nusar da dukkanin jam’iyyun siyasa su gano sahihan yan takara wadanda za su iya wakiltan mutane a dukkan matakai. An tattaro cewa mambobin kwamitin na a fadin jihohin arewa maso yamma.”

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An kashe mutum 7 tare da kona gidaje a sabon harin Kaduna

A wani labarin, Kingsley Fanwo, kwamishinan labarai da sadarwa na jihar Kogi, ya bayyana cewa Gwamna Bello na fuskantar matsin lamba kan ya fito takarar shugaban kasa a 2023.

Fanwo ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.

Sai dai kuma yan Najeriya sun bayyana cewa gwamnan bai isa hawa wannan babban matsayi a kasar ba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel