Martanin 'yan Najeriya a kan rahoton matsawa gwamna Bello ya nemi shugaban kasa a 2023

Martanin 'yan Najeriya a kan rahoton matsawa gwamna Bello ya nemi shugaban kasa a 2023

- Kingsley Fanwo, kwamishinan labarai da sadarwa na jihar Kogi, ya bayyana cewa Gwamna Bello na fuskantar matsin lamba kan ya fito takarar shugaban kasa a 2023

- Fanwo ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba

- Sai dai kuma yan Najeriya sun bayyana cewa gwamnan bai isa hawa wannan babban matsayi a kasar ba

Kwamishinan labarai da sadarwa na Kogi, Kingsley Fanwo, ya bayyana cewa mutane da dama sun bukaci gwamnan jihar, Yahaya Bello, da ya fito takarar shugaban kasa a 2023.

Legit.ng ta tattaro cewa a yanzu haka Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi na cikin mutanen da ke tashe a soshiyal midiya bayan furucin da Fanwo yayi a shafinsa na Twitter @KingsleyFanwo cewa mutane da dama sun bukaci gwamnan ya tsaya takara a zaben.

Kwamishinan a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, ya ce muradin yan Najeriya na samun kasa mai ingani ya yi daidai da na Bello, inda ya kara da cewa “don haka mun san cewa kiraye-kirayen zai kawo lokaci mai ma’ana ga kasarmu.”

Martanin 'yan Najeriya a kan rahoton matsawa gwamna Bello ya nemi shugaban kasa a 2023
Martanin 'yan Najeriya a kan rahoton matsawa gwamna Bello ya nemi shugaban kasa a 2023 Hoto: @GovernorBello
Asali: Twitter

Ya wallafa a twitter:

“Yana son Najeriya ta inganta. Yan Najeriya na so Najeriya ta inganta. Ya aikata a jihar Kogi. Don haka mun san cewa wannan kiraye kirayen zai kawo lokaci mai ma’ana ga kasarmu. Muna tunanin Najeriya.”

Da yake bayani kan dalilinsa na wallafa lamarin a Twitter, kwamishinan ya bayyana cewa yan Najeriya da dama na neman gwamnan ya fito takarar babban kujera a kasar.

Fanwo ya kara da cewa:

“Mutane na kiransa kan ya fito takarar shugaban kasa, amma bai fito karara ya fada mana ko zai amsa tayin da ake masa ba.

"A dukkanin yankunan kasar shida,muna da mutane da dama da ke kira gare shi a kan ya fito takara. Idan ka yi duba ga mutanen da ke kira gare shi, sun bazu a fadin dukkanin jam’iyyu ba wai APC kadai ba. Ya cancanta sosai, ya fada a rukunin mutanen da yan Najeriya ke muradi.”

Bello, wanda ke wa’adi na biyu a matsayin gwamna, ya kasance daya daga cikin gwamnonin Najeriya mafi karancin shekaru inda yake da shekaru 40 a 2015.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya jagoranci jana’izar manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Borno

Sai dai kuma, yan Najeriya sun yi sharhi a kan jawabin Fanwo kan yiwuwar Yahaya Bello ya nemi shugabancin kasa, inda suka bayyana hakan a matsayin was an kwaikwayo.

Wani mai amfani da shafin Twitter, @krativity, ya ce gwamnan ya gaza cika alkawaran zaben da ya daukarwa mutanen jihar Kogi.

Ya ce:

“Yan Najeriya ba za su iya jurewa irin koma baya, rashin manufofi da rigimar da ke afkuwa a jihar Kogi ba. Baka cika alkawari a karamar jiha kamar Kogi ba amma ka fara daukar alkawarin isarwa a matakin kasa dan Allah ka daina irin wannan tatsuniyar a wannan rana ta Asabar.”

A sharhinsa, @AbbeyBabsp1, ya ce gwamnan ya gaza kula da jihar Kogi cikin nasara balle har a kai ga jagorantar Najeriya.

Ya ce:

“A dukkanin wallafarka ban aminta da wannan ba kwata-kwata. Duk da kankantar jihar Kogi ya gaza kula da ita yadda ya kamata balle ma a zo kan Najeriya. Har yanzu @ProfZulum ke zarra a gwamnonin jam’iyyarku gaba daya duk da karancin lokacin da yayi a mulki da tarin matsalolin tsaron da jiharsa ke fuskanta.”

KU KARANTA KUMA: An yi nadin manyan muhimman sarautu guda 7 a masarautar Katsina

Wani mai amfani da Twitter, @adexzona, ya bayyana cewa shi zai so Bello ya tsaya takarar Shugaban kasa a 2023 domin gwada farin jininsa a cikin mutane.

A wani labarin, an gano Sanata Mohammed Ali Ndume a wajen wani taro a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba, a Abuja yan kwanaki bayan sakinsa daga gidan gyara hali.

Taron ya samu halartan tsohon Shugaban kasar Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan, wanda ya wallafa hotunan taron a shafinsa na soshiyal midiya.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel