Yanzu Yanzu: An kashe mutum 7 tare da kona gidaje a sabon harin Kaduna
- Wasu yan bindiga sun kai farmaki wani gari a karamar hukumar Jemaa da ke jihar Kaduna
- Maharan sun kashe mutum bakwai, sun raunata hudu sannan suka kona akalla gidaje hudu
- Harin na zuwa ne kimanin kwanaki hudu bayan yan fashi sun kashe wasu mutane hudu a Kaduna
Jihar Kaduna ta shiga juyayi bayan wani harin sassafe da aka kai sannan aka kashe akalla mutane bakwai a kauyen Ungwan Bido da ke karamar hukumar Jemaa.
Channels TV ta ruwaito cewa wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba wadanda suka far na kauyen a ranar Lahadi, 29 ga watan Nuwamba sune suka kaddamar da harin.
Har yanzu ba a ga wasu yara biyu ba bayan mummunan al’amarin yayinda maharan suka raunata mutum uku da kona gidaje hudu.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, wanda ya tabbatar da lamarin ya kuma bayyana cewa harin ya biyo bayan rahoton kisan wani Isiyaka Saidu.
KU KARANTA KUMA: Martanin 'yan Najeriya a kan rahoton matsawa gwamna Bello ya nemi shugaban kasa a 2023
An kashe Saidu wanda ya kasance makiyayi a kauyen Ungwan Pah a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.
A halin da ake ciki, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi martani kan sabon harin sannan yayi Allah-wadai da lamarin.
Yayinda yake jaje ga iyalan mamatan da wadanda aka raunata, gwamnan ya umurci hukumomin tsaro da su yi bincike da kamo dukkanin masu hannu a ta’asar.
KU KARANTA KUMA: Jam’iyyar PDP na shirin tarwatsewa yayinda karin wasu gwamnoni ke barazanar komawa APC
A wani labarin kuma, Gwamna Zulum ya jagoranci jana'izar manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Zabarmari da ke jihar Borno.
An tattaro cewa har yanzu ba a gama tantance adadin wadanda aka kashe ba da kuma wadanda suka bata.
A daren ranar Asabar ne dai maharan suka abka wa manoman yayin da suke girbin shinkafa kauyen Koshebe da ke karamar hukumar Mafa.
Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng