Jam’iyyar PDP na shirin tarwatsewa yayinda karin wasu gwamnoni ke barazanar komawa APC

Jam’iyyar PDP na shirin tarwatsewa yayinda karin wasu gwamnoni ke barazanar komawa APC

- An tattaro cewa wasu gwamnonin PDP na barazanar barin jam’iyyar zuwa APC

- Gwamnonin sun bukaci Shugaban jam’iyyar da ya mika tikitin takarar shugaban kasa zuwa kudu

- Kwanaki Gwamna Umahi ya koma APC duk a kan lamarin yankin da za a ba tikitin takara

Rashin sanar da yankin da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) za ta mikawa tikitin takarar shugaban kasarta a 2023, ya sa shugabannin jam’iyyar sun fara juyawa juna baya.

The Nation ta ruwaito cewa kwamitin masu ruwa da tsaki ta NWC na PDP na fuskantar matsin lamba domin kaddamar da matsayinsa kan tsarin mika mulki na yanka-yanka.

Legit.ng ta tattaro cewa karin gwamnoni da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar, suna barazanar sauya sheka idan shugabancin jam’iyyar ya ki nuna jajircewarsa wajen mika tikitin shugaban kasa ga yankin kudu.

Jam’iyyar PDP na shirin tarwatsewa yayinda karin wasu gwamnoni ke barazanar komawa APC
Jam’iyyar PDP na shirin tarwatsewa yayinda karin wasu gwamnoni ke barazanar komawa APC Hoto: @UcheSecondus
Source: Twitter

Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi, ya bayyana matsalar mika shugabanci ga yanki a matsayin dalilinsa na komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

KU KARANTA KUMA: Gwamna Zulum ya jagoranci jana’izar manoma 43 da Boko Haram ta yi wa yankan rago a Borno

Jaridar ta bayyana cewa majiyoyi sun ce shugaban PDP na kasa ya yanke shawarar tattaunawa da fusatattun jiga-jigan jam’iyyar bayan alamu sun nuna cewa jam’iyyar na iya fuskantar gagarumin sauya sheka idan har ba a magance lamarin ba cikin gaggawa.

Bayan matakin da Umahi ya dauka, jam’iyyar ta kira wani taro na gaggawa a Abuja.

Da yake magana a karshen taron, shugaban kungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, ya ce:

“Dukkaninmu mu 15 mun hallara a nan. Wannan ya nuna karara cewa akwai hadin kai a tsakaninmu sannan muna aiki don karfafa makomar jam’iyyarmu a gaba.”

A cewar jaridar, majiyoyi a taron sun ce wasu gwamnoni, yan majalisun tarayya da sauran jiga-jigan jam’iyyar musamman daga yankunan kudu uku, sun nuna rashin yardarsu a kan gazawar NWC na rashin tabbatar da shirin PDP na mutunta yarjejeniyar yankinsu a 2023.

Wata majiya ta ce:

“Taron NEC bai tafi daidai ba kamar yadda NWC ke sanar da jama’a. Lokaci ne da dukkaninmu za mu fuskanci zahirin gaskiya domin yawancin jiga-jiganmu daga kudu sun daura lefin guguwar sauya sheka da ke tunkarar jam’iyyar a yankin kan shirun shugabancin PDP kan muhawarar mulkin karba-karba.

KU KARANTA KUMA: An yi nadin manyan muhimman sarautu guda 7 a masarautar Katsina

“Gwamnoni da yan majalisu daga yankin sun bukaci shugabancin jam’iyyar da ya dauki matsaya kan lamarin domin dakatar da ci gaban sauye-sauyen sheka. Wasu adadi daga cikinsu sun bayyana cewa za su bar jam’iyyar idan ba a mika tikitin takara ga yankin kudu ba.”

An kuma tattaro cewa kwamitin NEC na jam’iyyar sun tashi ba tare da magance korafe-korafen fusatattun mambobin jam’iyyar ba.

A wani labarin, Kingsley Fanwo, kwamishinan labarai na jihar Kogi, ya bayyana cewa Gwamna Bello na fuskantar matsin lamba kan ya fito takarar shugaban kasa a 2023.

Fanwo ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 28 ga watan Nuwamba.

Don sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel