Za mu farauto makasan Shugaban APC na Nasarawa, Gwamna Sule ya sha alwashi

Za mu farauto makasan Shugaban APC na Nasarawa, Gwamna Sule ya sha alwashi

- Gwamnan jihar Nasarawa ya sha a alwashin zakulo yan bindigan da suka kashe shugaban APC na jihar

- A daren ranar Asabar ne makasan suka kai farmaki gidansa sannan suka tsere da shi

- An kuma tsinci gawarsa a safiyar ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba

Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa, ya bayyana cewa za a bankado makasan Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihar, Philip Shekwo.

Yan bindiga ne suka sace Shekwo daga gidansa da ke Lafia, babbar birnin jihar a daren ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba.

An tattaro cewa sun yi musayar wuta da jami’an tsaro da ke aiki da Shugaban na APC kafin suka tsere da shi.

Za mu farauto makasan Shugaban APC na Nasarawa, Gwamna Sule ya sha alwashi
Za mu farauto makasan Shugaban APC na Nasarawa, Gwamna Sule ya sha alwashi Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

Raman Nansel, kakakin yan sandan jihar Nasarawa, ya bayyana cewa an kashe Shekwo yayinda aka gano gawarsa a ranar Lahadi, 22 ga watan Nuwamba, jaridar TheCable ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Rahoto ya yi ikirarin cewa ana zawarcin Jonathan kan ya fito takara a APC

A wata sanarwa da ya saki da yawun Sule, babban sakataren labaran gwamnan, Ibrahim Addra, ya ce makasan Shugaban na APC ba za su ci bulus ba.

Ya ce za a yi farautar makasan sannan a hukunta su daidai da yadda doka ta tanadar.

“Mun sami labarin kisan Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress na jihar Nasarawa, Philip Tatari Shekwo, cike da alhini da wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka yi, bayan sun shiga gidansa ta karfin tuwo a daren jiya,” in ji sanarwar.

“Addu’ata da tunanina na tare da iyalan marigayi Shekwo. Ya kasance miji nagari, jigo, salihin mutum mai kuma biyayya ga jam’iyya.

“Ina son bayan da tabbacin cewa makasan sa ba za su ci bulus ba. Tuni jami’an tsaronmu suka fara gudanar da bincike a kan lamarin domin gano masu laifin da kuma hukuntasu.”

KU KARANTA KUMA: 2023: Dattawan arewa sun goyi bayan shugabancin Igbo

Jaridar Thisday ma ta ruwaito cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Abdullahi Sule sun sha alwashin tsamo makasan Shugaban na APC a jihar Nasarawa.

A baya mun ji cewa, shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Philip Tatari Shekwo, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Emmanuel Bola Longe, wanda ya tabbatar da hakan a wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da jaridar Leadership, ya ce 'yan bindiga masu tarin yawa ne suka tsinkayi gidan shugaban APC.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel