Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban APC a Nasarawa

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban APC a Nasarawa

- Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun shiga har gida tare da yin awon gaba da shugaban jam'iyyar APC a jihar Nasarawa

- Kamar yadda kwamishinan 'yan sandan jihar, Emmanuel Bola Longe ya sanar, lamarin ya faru wurin karfe 11 na daren Asabar

- Ya ce tuni jami'an tsaro suka gaggauta bazuwa a cikin dajin jihar domin tabbatar da sun ceto shugaban jam'iyyar

Shugaban jam'iyyar APC na jihar Nasarawa, Philip Tatari Shekwo, ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Emmanuel Bola Longe, wanda ya tabbatar da hakan a wata hirar wayar tafi da gidanka da yayi da jaridar Leadership, ya ce 'yan bindiga masu tarin yawa ne suka tsinkayi gidan shugaban APC.

KU KARANTA: EndSARS: Na kwashe wata 7 a gidan yari a kan tambayar dan sanda kudin mota, Direban Tasi

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban APC a Nasarawa
Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban APC a Nasarawa. Hoto daga @LeadershipNGA
Asali: Twitter

Gidan na kusa da cocin Dunamis da ke Bukan Sidi a Lafia. Sun isa gidan wurin karfe 11 na dare inda suka yi awon gaba da shi.

Longe ya tabbatar da cewa hukumar tsaro sun gaggauta daukar mataki ta hanyar tura jami'ansu wurare mabanbanta a dajin jihar domin tabbatar da an ceto shugaban jam'iyyar.

KU KARANTA: ASUU ta musanta komawa aiki, ta sanar da ranar cigaba da tattaunawa da FG

A wani labari na daban, direbobin motocin haya, masu zuwa Abuja zuwa Kaduna sun koka a kan yadda fasinjoji suka gwammaci bin jirgin kasa a kan motoci, saboda tsoron fadawa hannun 'yan bindiga.

Jaridar Daily trust ta bayyana yadda garkuwa da mutane ya yawaita a wurin 200km na babban titin, cikin 'yan kwanakin nan.

Wani direban garejin Zuba, Abdulsalam Abubakar, wanda kullum cikin bin hanyar Abuja zuwa Kaduna yake, ya ce rashin yawan fasinjojin ya fara ne tun daga lokacin da garkuwa da mutane ya fara zama ruwan dare.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel