2023: Dattawan arewa sun goyi bayan shugabancin Igbo

2023: Dattawan arewa sun goyi bayan shugabancin Igbo

- Gabannin zaben 2023, ana ta kiraye-kiraye a kan goyon bayan shugabancin Igbo

- Kungiyar dattawan arewa masu son zaman lafiya da ci gaba na daya daga cikin masu goyon bayan Shugaban kasa dan kabilar Igbo

- Dattawan na arewa sun ce lallai ya kamata a mika tikitin Shugaban kasa na 2023 zuwa kudu maso gabas

Yayinda aka fara kamfen a kan zaben Shugaban kasa na 2023, kungiyar dattawan arewa masu son zaman lafiya da ci gaba sun fara goyon bayan shugabancin kabilar Igbo.

A wani rahoto da jaridar Leadership ta wallafa, dattawan arewan sun bayyana cewa lallai ya kamata a mika wa yankin kudu maso gabashin Najeriya shugabancin kasar a 2023 ba wani wani yanki daban ba.

Dattawan sun bayyana matsayinsu a cikin wata sanarwa daga shugabansu na kasa, Injiniya Zana Goni da Hajia Mario Bichi, shugabar mata ta kasa.

2023: Dattawan arewa sun goyi bayan shugabancin Igbo
2023: Dattawan arewa sun goyi bayan shugabancin Igbo Hoto: @APCNigeria
Asali: Twitter

Sun bayyana cewa ya kamata shugaban kasar na gaba ya kasance Igbo sannan sun bayar da shawarar cewa a ci gaba da tsarin tsarin karba-karba tsakanin arewa da kudu.

KU KARANTA KUMA: Rahoto ya yi ikirarin cewa ana zawarcin Jonathan kan ya fito takara a APC

A cewar dattawan arewan, mulkin karba-karba ya taimaka wajen rage tashin hankali a Najeriya.

Yayinda suke bayyana cewa matsayarsu ya fito ne daga bukatar son ganin an yiwa dukkanin yankunan Najeriya adalci a lamuran siyasar kasar, kungiyar dattawan sun ce a mayar da Igbo saniyar ware a tsarin yin abubuwa.

Dattawan sun yi kira ga jam’iyyun All Progressives Congress, (APC) da Peoples Democratic Party, (PDP), a kan su cike gurbin yan takara daga kudu maso gabas.

A bangare guda, dattawan na arewa sun roki dukkanin yankunan kasar a kan su marawa Igbo baya a fafutukarsu na son samar da Shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Ziyarar gwamonin APC ga Goodluck Jonathan: PDP ta yi martani

A gefe guda, Ambasada Yahaya Kwande, jigon kungiyar dattawan arewa, ya nemi PDP ta mika tikitinta ga yankin arewacin kasar a 2023.

Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa tsohon jakadan na Najeriya a kasar Switzerland, ya yi bayanin cewa tsarin karba-karba baya cikin gudun tsarin mulkin kasar, cewa tsari ne na jam’iyyun siyasa don magance wasu matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel