Rahoto ya yi ikirarin cewa ana zawarcin Jonathan kan ya fito takara a APC
- Wani rahoto ya yi ikirarin cewa yan siyasa a APC na kokarin neman dan takarar Shugaban kasa da ya kamata gabannin zaben 2023
- Wata jaridar kasar ta ruwaito cewa ziyarar da gwamnonin APC suka kai wa tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan na siyasa ne
- Ziyarar da gwamnonin na APC suka kai masa ya kuma haifar da rade-radin shugabancin Jonathan a 2023
Wani rahoto da ya billo ya yi ikirarin cewa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na zawarcin tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan, domin ya fito takarar Shugaban kasa a inuwarta a 2023.
Rahoton wanda jaridar This Day ta kawo ya yi ikirarin cewa wasu shugabannin jam’iyyar na matsawa tspohon Shugaban kasar a kan ya duba yiwuwar amsa tayin.
Jaridar ta bayyana cewa wata majiya wacce ta nemi a boye sunanta ta ce gwamnonin APC wadanda suka ziyarci Jonathan don taya shi murnar cika shekaru 63, sun yi amfani da taron wajen yi masa tayin kujerar shugabancin kasar.
Rahoton ya ci gaba da ikirarin cewa makusantan Buhari na goyon bayan yunkurin ganin Jonathan ya zama Shugaban kasa a 2023.
KU KARANTA KUMA: An sako daliban ABU 9 da aka yi garkuwa da su
A cewar ikirarin, makusantan Buhari sun yarda cewa Jonathan ba zai cutar da ra’ayin kungiyarsu ba saboda haka shine ya cancanci karban mulki idan aka mika ta kudu.
Wata majiya a sansanin Buhari wacce bata so a bayyana ta tace:
“Ya mika mulki cikin lumana sannan bai riki kowa ba saboda haka ba zai zama barazana ga ra’ayin arewa ba.”
Sai dai, a baya Jonathan ya sha karyata cewar yana da ra’ayin takarar Shugaban kasa. Tsohon Shugaban kasar ya bayyana arara cewa ya mayar da hankalinsa ne a kan gidauniyarsa.
A gefe guda, Ambasada Yahaya Kwande, jigon kungiyar dattawan arewa, ya nemi PDP ta mika tikitinta ga yankin arewacin kasar a 2023.
KU KARANTA KUMA: An kama wasu mutane biyu da suka yi wa dan sanda gashin tsire tare da cin namansa
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa tsohon jakadan na Najeriya a kasar Switzerland, ya yi bayanin cewa tsarin karba-karba baya cikin gudun tsarin mulkin kasar, cewa tsari ne na jam’iyyun siyasa don magance wasu matsalolin da Najeriya ke fuskanta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng