Dattijon arewa, Kwande, ya bayyana dalilin da zai sa shugaban kasa ya sake fitowa daga yankin
- Ambasada Yahaya Kwande ya bayyana cewa ya kamata arewa ta samar da Shugaban kasar Najeriya na gaba
- A cewar tsohon jakadan na Najeriya, ya kamata PDP ta mika shugabancin kasa zuwa yankin arewa a 2023
- Kwande ya bayyana cewa tsarin mulkin karba-karba da jam’iyyu ke yi ya kasance yarjejeniyarsu don magance wasu matsalolin siyasa a kasar
A yayinda ake tsaka da tattaunawa kan wanda zai karbi mulki daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ambasada Yahaya Kwande, jigon kungiyar dattawan arewa, ya nemi PDP ta mika tikitinta ga yankin arewacin kasar a 2023.
Jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito cewa tsohon jakadan na Najeriya a kasar Switzerland, ya yi bayanin cewa tsarin karba-karba baya cikin gudun tsarin mulkin kasar, cewa tsari ne na jam’iyyun siyasa don magance wasu matsalolin da Najeriya ke fuskanta.
Kwande da yake zantawa da jaridar a Jos ya kuma bayyana cewa PDP ta fara mulkin karba-karba don tausar yankin kudu bayan soke zaben ranar 19 ga watan Yuni, 1993.
A cewarsa, tsohon Shugaban kasa Goodluk Jonathan ya hana arewa damar kammala wa’adin mulkinsa na shekaru takwas bayan ya yi takarar zabe a 2011.
KU KARANTA KUMA: An sako daliban ABU 9 da aka yi garkuwa da su
“Ya fara ne a PDP, mulkin karba-karba baya cikin kundin tsarin mulkin kasarmu, yarjejeniyar jam’iyya ne. Kudu ta samar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo na tsawon shekaru takwas, bayan nan sai arewa ta samar da Shugaban kasa, marigayi Umar Yar’adua amma bai kammala wa’adin mulkinsa na farko ba saboda rasuwa da yayi. Mataimakinsa, Goodluck Jonathan ya kammala kamar yadda kundin tsarin mulki ta tanadar.
“Maimakon Jonathan ya bari wani dan arewa ya yi takara a 2011, sai ya yi takara sannan ya ci, don haka ya tauyewa arewa damarta na kammala shekaru takwas. Saboda haka, bisa tsarin karba-karba na PDP, har yanzu arewa na da sauran shekaru hudu.
“Manufar mulkin karba-karbatsari ne na jam’iyyun siyasa, idan har PDP ba za ta yi son kai ba a 2023, har yanzu arewa na da sauran shekaru hudu saboda tsohon Shugaban kasa Goodlluck Jonathan ya karbe mata shekaru hudunta. Tambayar cewa Buhari dan arewa ne baya da amfani, dan wata jam’iyyar siyasa ne, mulkin karba-karba lamari ne na jam’iyya,” in ji shi.
KU KARANTA KUMA: An kama wasu mutane biyu da suka yi wa dan sanda gashin tsire tare da cin namansa
A wani labarin, Obinna Oriaku, tsohon kwamishinan kudi a jihar Abia, ya yi murabus daga babbar jam’iyyar adawa ta kasar wato Peoples Democratic Party (PDP).
An rahoto cewa Oriaku ya sanar da shawarar da ya yanke ne a cikin wata wasika da ya gabatarwa da Shugaban PDP na gudunmarsa, Mbutu Ukwu Ward 3, Isiala Ngwa South, Owerrinta.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng