An kama wasu mutane biyu da suka yi wa dan sanda gashin tsire tare da cin namansa

An kama wasu mutane biyu da suka yi wa dan sanda gashin tsire tare da cin namansa

- Rundunar yan sanda ta damke wasu mutane biyu da ake zargi da yi wa dan sanda gashin tsire

- An kuma zarge su da cin naman jami'in tsaron bayan sun gasa shi

- Kakakin rundunar yan sandan jihar Oyo ya tabbatar da kamun nasu inda yace an tura su zuwa hedkwatar rundunar da ke Abuja don ci gaba da bincike

Rundunar yan sandan jihar Oyo a ranar Asabar, 21 ga watan Nuwamba, ta bayyana cewa ta tsare wasu mutum biyu da ake zargi da gasawa tare da cin naman jami’in dan sandan da aka kona a Ibadan a lokacin zanga zangar EndSARS.

Kakakin rundunar yan sandan na jihar Oyo, SP Olugbenga Fadeyi, ya tabbatar da kamun a Ibadan a yayinda yake zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya.

Ya ce an tura wadanda ake zargin da suka hada da mai ciki yar shekaru 34 da wani mai shekaru 43 zuwa ga sashin kwararru a hedkwatar rundunar da ke Abuja domin ci gaba da bincike.

KU KARANTA KUMA: An shiga har cikin Caji Ofis an harbe dan sanda a Ofishinsu da ke Ado

An kama wasu mutane biyu da suka yi wa dan sanda gashin tsire tare da cin namansa
An kama wasu mutane biyu da suka yi wa dan sanda gashin tsire tare da cin namansa Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

An yi zargin cewa matar mai shekaru 34 ta ci wasu sassa na jikin daya daga cikin yan sandan da aka babbake, lamarin da ta karyata.

Ta ce da gaske tana a wajen da abun ya faru, cewa mutum na biyu da ake zargi mai shekaru 43 ne ya bata naman ta ajiye masa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Shima mutumin mai shekaru 43 bai karyata batun kasancewa a wajen da lamarin ya afku tare da sauran yan iskan ba, amma ya ce matar ce ta dauki sassan jikin da kanta.

Ya jadadda cewa kawai ta nemi ya bata kyalle ne domin ta rufe shi.

Jami’an yan sandan da aka kashe, an tura su wajen ne domin su kula da zanga zangar EndSARS na ranar 22 ga watan Oktoba, wanda yan iska suka janye ragamar gangamin.

KU KARANTA KUMA: 'Yan bindiga sun kashe shugaban PDP a Katsina

A gefe guda, wasu 'yan sanda da 'yan sa kai da ke Ogwashi-Uku, karamar hukumar Aniocha ta kudu da ke jihar Delta, sun kama wasu samari 2 da akwatin gawa, cike da 'yan kamfan mata da rigunan nono.

An kama wadanda ake zargin a wuraren Agidiehe quarters da misalin karfe 9:30 na daren Laraba, kamar yadda labarai suka bayyana. Sai da 'yan sa kai suka kama su tukunna aka sanar da 'yan sanda.

Kamar yadda wata majiya ta sanar, hankulan mata da samarin yankin sun yi matukar tashi sakamakon aika-aikan 'yan damfarar yanar gizon.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel