Fadar Shugaban kasa ta yi nadamar rashin samun damar zama da gwamnoni

Fadar Shugaban kasa ta yi nadamar rashin samun damar zama da gwamnoni

- Muhammadu Buhari ya bayyana abin da ya hana shi zuwa Jihar Ribas jiya

- An shirya cewa shugaban kasar zai gana da shugabannin yankin Neja-Delta

- A karshe dole aka fasa zaman inda shugaban kasar ya gana da hasfun tsaro

A ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, 2020, fadar shugaban kasar Najeriya ta ce ta yi nadamar rashin ganawa da duk gwamnonin Kudu maso kudu.

An tsara cewa shugaba Muhammadu Buhari zai yi taro da gwamnonin yankin Kudu maso kudu a garin Fatakwal, amma a karshe Ubangiji bai nufa ba.

Shugaban kasar ya ce wani taron gaggawa da ya shiga tare da shugabannin majalisar tsaro ya sabbaba rashin halartar zamansa da gwamnonin kasar.

KU KARANTA: Kano ta fi kowace Jiha yaki da rashin gaslkiya - Ganduje

Mai magana da yawun bakin shugaban kasa, Garba Shehu ya bada uzuri na kin halartar zama da Gwamnonin, jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto.

Shugaban kasar ya ce taro ne ya fado masa kwatsam a fadar Aso Rock Villa a kan harkar tsaro.

Mai girma Muhammadu Buhari ya ce za a sake samun rana ta musamman da za a rama wannan zama. Za a sa ranan ne bayan la’akari da wasu batutuwa.

Gwamnoni da shugabannin yankin Kudu maso kudu sun bukaci shugaban kasar ya fito gaban Duniya ya ba su hakuri na bata masu lokaci da aka yi a banza.

KU KARANTA: Tsofaffin Kansilolin Zamfara sun koma PDP

Fadar Shugaban kasa ta yi nadamar rashin samun damar zama da gwamnoni
Gwamnonin Kudu maso Kudu Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Garba Shehu ya ce har tawagar shugaban kasar ta fara shirin tafiya Fatakwal, sai aka dakatar da ita, saboda taron gaggawar da Buhari ya shiga a fadar Aso Villa.

“Har ila yau, an yi nadamar dage wannan zama bayan abin ya zama dole.” Inji Garba Shehu.

Dazu kun ji cewa, Mohammed Umar Bago ya tube rigar siyasa a gefe, ya soki salon-mulkin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba a a fada masa gaskiya.

Sannu a hankali, jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki su na kuka da halin da ake ciki a kasa.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://facebook.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel