Zamfara: Tsofin Kansiloli 69 tare da magoya bayansu sun sauya sheka zuwa PDP
- Wasu gungun tsofin kansiloli har su 69 tare da magoya bayansu sun dunguma sun koma jam'iyyar PDP a jihar Zamfara
- Jamilu Iliyasu, sakataren yada labaran gwamna Bello Matawalle, ya ce tsofin kansilolin sun yi mulki a tsakanin 2012 zuwa 2019
- Sauyin shekar kansilolin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cece-kuce a kan komawar gwamna Dave Umahi na Ebonyi jam'iyyar APC
A kalla tsofin kansiloli 69 ne daga kananan hukumomi 14 a jihar Zamfara suka sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP, kamar yadda Punch ta rawaito.
Hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da Jamilu Iliyasu, sakataren yada labaran gwamna Bello Matawalle, ya fitar a ranar Talata.
Ya ce tsofin kansilolin, wadanda suka yi mulki a tsakanin 2012 zuwa 2019, sun hada kansu a karkashin kungiya guda kafin su dunguma zuwa cikin jam'iyyar PDP.
KARANTA: Trump ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe halastaccen zaɓe a Amurka
Shugaban kungiyar tsofin kansilolin, Tukur Magami, ya ce sun yanke shawarar komawa jam'iyyar PDP ne saboda gamsuwarsu da salon mulkin gwamna Matawalle.
A cewarsa, gwamnati, irin ta Matawalle, mai kishin jama'a, ta na bukatar gudunmawa da goyon baya domin samun damar cigaba da ayyukan alheri.
KARANTA: 'Yan bindiga sun sace ASP 12 daga tawagar 'yan sanda a tsakanin Katsina da Zamfara
A nasa jawabin, Matawalle ya nuna jin dadinsa tare da yin Kira ga duk masu kishin Zamfara da jama'ar ta a kan su hada kai da shi domin ciyar da jihar gaba.
Sauyin shekar kansilolin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da cece-kuce a kan ficewar gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, wanda ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a cikin makon nan.
Legit.ng ta rawaito cewa Umahi, a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba, ya ce ya zama abun zargi a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) saboda kawai ya ki caccakar Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng