Ganduje: Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano ta fi kowacce tasiri a Nigeria

Ganduje: Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano ta fi kowacce tasiri a Nigeria

- Gwamna Abdullahi Ganduje ya jinjinawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano

- Ganduje ya ce hukumar ta jihar ta fi kowacce tasiri da karfi a Najeriya

- A cewar gwamnan, wasu kwamishinoni da manyan jami'an gwamnatin jihar sun rasa aikinsu saboda aikin hukumar ta yaki da rashawa

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar, ita ce mafi karfi a kasar nan wajen inganta lissafin kudaden jama’a da kuma jagoranci nagari.

Ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na kungiyar akawun Najeriya (ANAN) wanda aka gudanar a Nassarawa GRA, Kano, a ranar Talata, 17 ga watan Nuwamba.

KU KARANTA KUMA: Hotunan Bashir El-Rufai da amaryarsa ya janyo cece-kuce

Ganduje: Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano ta fi kowacce tasiri a Nigeria
Ganduje: Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano ta fi kowacce tasiri a Nigeria Hoto: @bbc
Asali: Twitter

“A Kano muna da hukumar yaki da cin hanci mafi tasiri. Sakamakon aikin hukumarmu ta yaki da cin hanci da rashawa, wasu kwamishinoni sun rasa ayyukansu. Haka ma wasu sakatarorin din-din-din da daraktan ma’aikatar gwamnatin jihar suka rasa ayyukansu.

“Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) da sauran hukumomin yaki da rashawa ta tarayya ne suka horar da ma’aikatan hukumarmu ta yaki da rashawa. Saboda su samu gogewa ta zamani wajen yaki da rashawa,” in ji shi.

Gwamnan ya yaba ma kungiyar akawun, cewa aikinsu mai rai ne sannan ya bukace su da su ci gaba da hada kansu da karfafa kansu, Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Zunubina guda a PDP shine cewa na ki matsawa Buhari, Gwamna Umahi

A nashi jawabin, Shugaban kungiyar, Farfesa Muhammad Akaro Mainoma ya yi godiya ga gwamna Ganduje a kan inganta Kano da yayi.

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu fastoci 42 da kuma manyan limaman bishop biyu tare da iyalansu sun amshi addinin musulunci.

An yi taron musuluntar da su ne a dakin taro na babban masallacin kasa da ke birnin tarayya Abuja.

An kuma gudanar da taron kara ma juna sani na tsawon kwanaki bakwai domin wayar masu da kai a kan shika-shikan addinin Musulunci.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng